Zidane Ya Musanta Barin Real Madrid

- Advertisement -

Zidane Ya Musanta Barin Real Madrid

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Zinadine Zidane, ya musanta rahotannin da ake ci gaba da yadawa kan cewar ya shaidawa ‘yan wasansa aniyarsa ta ajiye aikinsa a karshen kakar wasa ta bana.

A cewar Zidane ba zai taba shaidawa ‘yan wasansa irin wannan magana ba, kuma ma a yanzu haka batun samun nasarar lashe kofin La Liga na bana shi ne abinda suka sanya a gaba, amma ba makomar aikinsa na horar da kungiyar Real Madrid ba.

Martanin Zidane ya zo ne kasa da mako daya, bayan da rahotanni suka ce  bayan kammala wasan da suka tashi 2-2 da kungiyar kwallon kafa ta Sebilla a makon jiya, kocin ya shaidawa ‘yan wasansa ba zai ci gaba da horar da ita ba a kakar wasan dake tafe.

Duk da cewar Real Madrid ta doke Athletic Bilbao da 1-Zero a jiya Lahadi, har yanzu suna fuskantar barazanar kammala kakar wasa ta bana ba tare da lashe kofi ba, la’akari da cewar akwai tazarar maki biyu tsakanin ta da Atletico Madrid.

Tuni dai aka fara alakanta tsohon dn wasan kungiyar ta Real Madrid, Raul Gonzales dam aye gurbin Zidane sannan shima tsohon kociyan Jubentus, Madimilliano Allegri ana ganin zai iya karbar aiki daga hannun Zidane.

- Advertisement -