Zargin Tsana: Martani Mai Gauni Da Jonathan Ya Mayar Wa el-Rufai

- Advertisement -

Zargin Tsana:  Martani Mai Gauni Da Jonathan Ya Mayar Wa el-Rufai

Daga Khalid Idris Doya

 

Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Ebele Jonathan, ya maida wa Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai martani mai gauni dangane da zarginsa da ya yi na cewa ya tsaneshi ne don yana tunanin shi babban barazana ne a gare shi a siyasance.

Jonathan ya ce el-Rufai ya kullace shi a rai ne kawai sakamakon neman ya jawo shi a jika tare da mara masa baya da bai yi ba, ya kuma ce el-Rufai ya fara fusata ne tun lokacin da Jonathan din ya zabi Namadi Sambo a matsayin mataimakinsa a yayin zaben 2011.

A sanarwar da mai magana da yawun Jonathan, Reno Omokri ya fitar, ya misalta Gwamnan Kaduna a matsayin mai surutan da suka saba wa gaskiya kuma wanda ya gaza rike amanar siyasa.

Reno Omokri na cewa: “Hankali ya karkata kan zargin da Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir el-Rufai ya yi na cewa wai an tsane shi a zamanin mulkin Dakta Goodluck Jonathan ne domin tunanin shi ne zai iya amsar mulki daga hannun Jonathan wato shi barazana ne gare shi.”

Reno ya ce, babu wani abun da zai iya jinkirta gaskiya, yana mai cewa a kowani lokaci gaskiya sunanta gaskiya ta bayyana a halin yanzu.

Ya cigaba da cewa: “’Yan Nijeriya za su iya tunawa, el-Rufai bisa kashin kansa ya zabi yin gudun hijira a zamanin mulkin Shugaban Kasa Umar Musa Yar’adua. Kuma el-Rufai ya dawo gida Nijeriya a ranar 5 ga watan Mayun 2010, rana guda da shugaban kasa ‘Yar’adua ya rasu.

“Ya dawo ne a lokacin da ya yi amanar yanayin kasar ya fi masa kyau da aminci a karkashin Jonathan. Hakan ya kuma samu asali sakamakon yarda da gamsuwa da ya yi na cewa Jonathan adali ne kuma mai gaskiya wanda ba zai cutar da shi ba.”

Kakakin na Jonathan ya fayyace hakikani kuma musabbabin fara samun takun saka a tsakanin Jonathan da el-Rufai, inda ya yi bayanin cewa “Kwana shida bayan dawowar El-Rufai ya kutsa fadar shugaban kasa ya ziyarci shugaban kasa Jonathan a fadar a ranar 11 ga watan Mayun 2010, bayan da ya fito ya gana da ‘yan jarida ya fito ya sharara son zuciyarsa, ya danganta da cewa wai Dakta Jonathan ya amince zai mara wa da goya masa baya a zaben 2011.

“Bayan da shugaban kasa ya ayyana sunan Malam Namadi Sambo a matsayin mataimakinsa, kwanaki biyu bayan an yi wannan, el-Rufai ya fusata matuka ya kuma shirya ficewa daga jam’iyyar PDP nan take kuma ya fara adawa da sukar gwamnatin Jonathan.”

Sanarwar ta kara da cewa, “Shi Jonatahan ya taba fada cewa ‘Ba ni da abokan gaban yin fada, saboda na yi amannar mutane kawai za su iya abun da Allah ya amince musu a kaina ne,” furucin da Jonathan ya yi a kokarinsa na kauce wa biye wa el-Rufai a wancan lokaci.

Sanarwar ta zargi el-Rufai da cewa a wancan lokacin daga cikin matakan da ya dauka har da kokarin tada zaune tsaye da neman haddasar da fitina domin neman suna da shiga, “Ya yi ta sharara maganganu na kage domin ya tayar da hankali a kasa da neman tarwatsa zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da neman jawo zagon kasa wa cigaban kasa, sannan ya yi kokarin jawo nakasu ga alakar kasashe makwafta, dukka ya yi wadannan ana kallonsa a zamanin Jonathan. Daga cikin irin wadannan maganganu da el-Rufai ya yi har da cewa Jonathan ne ya kafa kungiyar Boko Haram kuma ya tallafa musu da Naira Biliyan 50.”

Mista Reno ya cigaba da zayyano zarginsu ga el-Rufai, kamar haka: “Kuma (el-Rufai) ya taba bayyanawa a ranar 25 ga watan Nuwamban 2014 cewa Jonathan ya je Chadi domin tsara yadda ‘yan Boko Haram za su kai hari wa marigayi shugaba Deby. Sannan, a ranar 5 ga Janairun 2014 ya sake cewa shi da Janar Buhari da wasu fitattun mutane gwamnatin Jonathan ta shirya kashe su.”

“Dukka wadannan zarge-zarge da shata magnganu da el-Rufai ya dinga shararawa solar kai matsayin laifin da ya kamata gwamnatin Jonathan ta kama shi ta kuma daure shi ta gurfanar da shi a gaban shari’a, amma Jonathan ya kau da kansa daga hakan domin kauce wa jawo tashin hankalin siyasa a kasar nan.”

Mutanen Jonathan din solar zargi el-Rufai da kasancewa batulu wanda a kowani lokaci ya saba juyawa da cin amanar wadanda suka tallafa masa da taimakonsa a rayuwa musamman a siyasance.

Ya kuma kara kafa hujja da neman gamsar da ‘yan Nijeriya cewa Gwamnan Kaduna, “Mai maganganu ne da ba na gaskiya ba, domin a shafi na 272 na littafin ‘Energy, Politics and Loss of life: A Entrance-row Account of Nigeria Beneath the Late President Umaru Musa Yar’Adua’, wanda tsohon Editan jaridar ThisDay kuma kakakin Shugaban kasa Yar’adua, Segun Adeniyi ya rubuta, ya bayyana el-Rufai a matsayin makaryaci.”

“A karshe an bayyana el-Rufai a matsayin mai maganganu kuma maciyin amana kamar yadda tsohon uban gidansa a siyasa, Alhaji Atiku Abubakar ya nuna shi, wanda ya sanshi ya kuma jawo shi cikin gwamnatin Obasanjo, amma daga baya ya zo ya kware masa baya.

“A bisa irin wadannan munanan dabi’u da halayen tir na irin wannan mutanen, ‘Yan Nijeriya ba za su taba shan mamaki da irin wadannan maganganun da el-Rufai ya sharara ba.”

Daga karshe dai Kakakin Jonathan din, Mista Reno Omokri, ya bukaci ‘yan Nijeriya da su cigaba da addu’ar neman zaman lafiya da cigaban kasa tare da daurewarta.

Idan za ku iya tunawa dai LEADERSHI A YAU ta ranar Alhamis da ta gabata, ta buga labarin yadda Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmed el-Rufai ke zargin cewa, tsofaffin  shugabanin Nijeriya Umaru Musa Yar’Adua da kuma Goodluck Jonathan solar tsane shi ne saboda solar dauke shi a matsayin barazana a gare su.

Ya ce,  Yar’Adua ya ci zarafinsa saboda yana ganin tsohon shugaban kasa  Cif  Olusegun Obasanjo na son ya sa shi a matsayin wanda zai gaji kujerarsa.

Hakazalika,  bayan rasuwar Yar’Adua a ranar 5 ga watan Mayun shekarar 2010, Jonathan ya dare kan karagar shugaban kasa .

Gwamna el-Rufai a cikin hirar ya bayyana cewa,  Yar’Adua ne ya fara tsanar sa, inda kuma Jonathan ya dora daga inda marigayi Yar’Adua ya tsaya.

A cewarsa, “Shi ma Jonathan ya aminta da cewa,  ni kalubale ne a gare shi,  in har kuma yana son yin tazarce karo na biyu, dole ne ya san dukkan yadda zai yi domin ya dakatar da ni daga yin takara”.

Malam ya ci gaba da cewa,  “Hakan ne ya  sa Jonathan ya ci gaba da kyarata daga inda marigayi Yar’adua  ya faro.”

Malam ya yi nuni da cewa,  hakan na daya daga cikin dalilin da ya sa  ya arce daga Nijeriya don yin gudun hijira.

- Advertisement -