Zargin Da Ake Wa Kasar Sin Na Kisan Kiyashi A Xinjiang Ba Shi Da Tushe

0
60

Zargin Da Ake Wa Kasar Sin Na Kisan Kiyashi A Xinjiang Ba Shi Da Tushe

Daga CRI Hausa

Wasu masana solar bayyana cikin wani sharhin da suka rubuta cewa, zargin da ake kira da “kisan kiyashi” a Xinjiang ba shi da tushe naked makama, don haka ya kamata Amurka ta janye wannan zargin.
Jeffrey D. Sachs, Daraktan cibiyar nazarin ci gaba mai dorewa ta Jami’ar Columbia da William Schabas, Farfesa a fannin Shari’a a Jami’ar Middlesex ta London, solar yi ittifaki cikin sharhin da kafar yada labarai ta Mission Syndicate ta fitar a makon da gabata cewa, zargin kisan kiyashi a Xinjiang ba shi da tushe.
Sharhi ya ruwaito cewa, Gwamnatin Amurka na ta yayata jita-jita kan kasar Sin, inda take ikirarin ana yi wa ‘yan kabilar Uygur kisan kiyashi, yana mai cewa, Amurkar bata da wata hujja.
Shehunan malaman solar kuma yi gargadin cewa, bai kamata a rika wasa da zargin kisan kiyashi ba, suna cewa, bai dace a yi amfani da kalmomin da ka iya kara zaman dardar dangane da harkokin siyasa da ayyukan soji ba. (Fa’iza Mustapha)

What's On Your Mind?