Zanga-zangar Kaduna: el-rufa’i Ya Kori Dukkan Malaman Jinya Kasa Da Mataki Na 14

- Advertisement -

Zanga-zangar Kaduna: el-rufa’i Ya Kori Dukkan Malaman Jinya Kasa Da Mataki Na 14

Daga Sulaiman Ibrahim

A yayin yajin aikin da ake yi don sanya Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, janye sallamar ma’aikata, gwamnan a yau Talata ya sanar da korar dukkan ma’aikatan jinya kasa da mataki na 14.

Matakin na gwamnan yana da nasaba da wani rubutu da yayi a kafar sadarwarsa ta tiwita, inda yake bayyana cewa asibitin Koyarwar na Barau Dikko ya bayar da rahoton cewa ma’aikatan jinya solar katse iskar numfashi daga wani jariri dan kwana biyu da haihuwa a ranar Litinin, 17 ga Mayu, 2021 lokacin da suka shiga yajin aikin kungiyar kwadago.

A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai da sadarwa, Muyiwa Adekeye ya fitar, El-Rufai ya ce, “Baya ga mika ma’aikatan jinyar da suka katse igiyar numfashi ga dan jariri zuwa Ma’aikatar Shari’a don fara gabatar da kara, gwamnatin ta kuma sanar da korar dukkan ma’aikatan jinyar da ke kasa da Mataki na 14. Saboda shiga yajin aiki ba bisa doka ba. ”

“An umarci Ma’aikatar Kiwon Lafiya da ta tallata guraben aiki don daukar sabbin ma’aikatan jinya cikin gaggawa don maye gurbin wadanda aka sallama.

“Gwamnati ta umarci dukkan ma’aikatun ta, sassanta da hukumomin su da su gabatar da rajistar halartar zuwa wajen aiki ga Shugaban Ma’aikata yayin da Jami’ar Jihar Kaduna ita kuma ta gabatar da rajistarta ga Sakataren Gwamnatin Jihar da Kwamishinan Ilimi.”

Adekeye ya kara da cewa za a bayar da albashin ma’aikatan jinyar da aka sallama ga wadanda basu shiga yajin aikin ba, suka tsaya a bakin aikin su a matsayin alawus na musamman.

Har yanzu kungiyar kwadago NLC ba ta mayar da martani sport da wannan sabon matakin da gwamnan ya dauka ba.

- Advertisement -