Zanga-zangar Iyayen Daliban Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kaduna Ta Nausa Majalisa

- Advertisement -

Zanga-zangar Iyayen Daliban Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kaduna Ta Nausa Majalisa

Daga Idris Aliyu Daudawa,

Iyayen daliban da aka sace na Kwalejin Nazari Al’amuran Gandun Daji ta Afaka da ke Jihar Kaduna, solar mamaye harabar majalisar dokoki ta kasa a Abuja, a lokacin da suka gudanar da zanga-zangar lumana.

Masu zanga-zangar, wadanda suka hada da mambobin kungiyar dalibai ta SUG na makarantar ta nuna alhininsu ne kan abin da suka bayyana da “sakacin gwamnatin Jihar Kaduna d kuma ta  tarayya wajen tabbatar da ganin ganin an sako daliban”.

Solar rera wakokin hadin kai tare da nuna alluna da suke bukatar a hanzarta ceto masu ‘ya’ya da abokansu daliban.

daliban solar bayyana cewa“Ilimi hakkinmu ne!  Kamar ma yadda shi tsaro hakkinmu ne da ya dace a bamu.

”Iyaye da daliban solar rera waka yayin da suke tafiya zuwa majalisar kasa.

Masu zanga-zangar, tare da mawallafin jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore da Deji Adeyanju, tun da farko solar hallara a Unity Fountain kafin su ci gaba da zuwa harabar majalisar dokoki ta kasa.

Sai dai kuma jami’an tsaro solar hana kowa samun hanyar shiga domin solar tar babbar hanyar shiga majalisar dokokin kasar.

A ranar 11 ga Maris 2021 ne, muka kawo maku rahoton cewar an sace dalibai 39 daga gidajen kwanan su dake cikin kwalejin.

 

- Advertisement -