Bidiyo: Zanga-Zangar EndSARS Shiri Ne Na Cin Mutuncin Buhari – Rashida Mai Sa’a

- Advertisement -

 

Finan Hausa ta Kannywood, ta ce suna goyon bayan Shugaban kasa Muhamamdu Buhari, domin zangar zangar da ake gudanar wa a yanzu wani shiri ne na cin mutuncin Shugaban kasar.

Jarumar wadda ake yi wa lakabi da Rashida Mai Sa’a, ta wallafa wani hoton bidiyo na tsawon mintuna 6 a shafinta na Instagram, inda ta bayyana cewa ana yi wa shugaba Buhari makarkashiya.

“Wannan zanga-zangar da ake yi akwai wata manufa a cikinta, duba da yadda aka ci gaba da tada hankalin mutane duk da cewa Shugaba Buhari ya soke rundunar ’yan sanda ta SARS”.

Zanga-Zangar EndSARS Shiri Ne Na Cin Mutuncin Buhari – Rashida Mai Sa’a

“A cikin tafiyar Shugaban Kasa, ’yan Arewa solar fi samun manyan gurabe duk da haka akwai wanda ake amfani da su wajen yi masa zangon-kasa”.

Rashida ta kara da cewa “ya kamata matasa su farga a daina amfani dasu wajen tada hankali, domin akwai wanda ba son ci gaban Najeriya suke ba”.

Bidiyo: kalli Yadda aka gwangwaje HAMISU BREAKER da kyautar Motoci Biyu Na Miliyan 5 Wajen Biki

A cikin bidiyon, Rashida ta bayyana cewa ’yan masana’antar Kannywood ba sa tare da wannan zanga-zangar ta #EndSARS da aka shirya.

A cewarta, duk dan Arewan da yake da kishi, tabbas ba zai goyi bayan zanga-zangar ba.

Ta kara da cewa mai dakin shugaban kasa, Aisha Buhari, ta sha yin kiraye-kiraye a baya domin a gyare-gyare a Gwamnatin Shugaban Kasa, amma wasu suka rinka ganin laifinta.

Ta ce “Aisha Buhari tana da gaskiya, domin ta san mutanen da ya kamata a ce an yi tafiyar gwamnati da su, wato wanda suka yi fadi-tashi a tafiyar Shugaba Buhari.

Rashida ta ce in har da gaske gyara ake bukata, kamata ya yi a zauna a teburin sulhu domin duba bukatun kowa ba wai a ringa tada hankalin jama’a ba.

Daga karshe ta ja hankalin Shugaba Buhari, a kan ya farga tare da yin gyara a cikin wanda yake tafiya dasu, inda tace akwai bara-gurbi, kuma dole sai ya sauya wanda suke masa zangon-kasa.

https://www.instagram.com/television/CGvGSmfhC2x/?utm_source=ig_embed&ig_mid=D165344F-FD96-41D1-82F1-9E6EF600D8D6

- Advertisement -