Zan Ci Gaba Da Tallafawa Real Madrid – Benzema

0
105

Zan Ci Gaba Da Tallafawa Real Madrid – Benzema

 

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Karim Benzema ya bayyana cewa zai ci gaba da tallafawa kungiyar wajen ganin ta samu nasara bayan ya ci gaba da kafa tarihi a wasannin da yake buga wa Real Madrid, wannan karon a fanni cin kungiyoyi 35 da ya hadu da su a gasar La Liga.

Ranar Talata Real Madrid ta doke kungiyar kwallon kafa ta Cadiz da ci Three-Zero a gasar La liga ta Spaniya, kuma Benzema ne ya ci biyu a karawar da ta kai ya zura kwallaye 21 jumulla a kakar wasan bana.

Wannan bajintar ta sa ya zama na farko da ya zura kwallo a dukkan kungiyoyi 35 da ya hadu da su a gasar La Liga sannan da wannan sakamakon Real Madrid ta koma ta biyu a kan teburin La Liga da maki 70 tazarar maki uku tsakaninta  da  Atletico Madrid wadda  ta karbi bakuncin kungiyar Huesca ranar Alhamis kuma ta doke ta.

Benzema ya buga wasanni 377 a La Liga a Real Madrid tun daga lokacin da ya fara yi mata wasa a ranar 29 ga watan Agustan shekara ta 2009 da ya fara cin kungiyar kwallon kafa ta Deportibo La Coruna.

“Real Madrid kungiya ce wadda b azan taba mantawa da irin kokarin da tayi min ba wajen ganin na zama babban dan wasa a duniya ta hanyar kafa tarihin lashe manyan kofuna da kuma buga wasa da manyan ‘yan wasa a duniya” in ji Benzema

Ya ci gaba da cewa “Zan ci gaba da dagewa wajen ganin wannan kungiya ta samu irin nasarar da ta cancanta ta samu wanda hakan wani aiki ne wanda na dorawa kaina kuma ina fatan zan sauke shi saboda ci gaban kungiyar shine ci gaban duk wani wanda yake tattare da kungiyar”

Kawo yanzu ya ci kwallo 190, shi ne na hudu a jerin wadanda suke kan gaba a ci wa Real Madrid kwallaye a tarihin gasar La Liga bayan Chritiano Ronaldo da Raul da kuma Alfredo de Stefano .

Kungiyoyi 35 da Benzema ya ci ko dai kwallo daya ko fiye da haka solar hada da Granada da Getafe da Malaga da Rayo da Athletic Bilbao da Betis da Sebilla da Barcelona da Real Sociedad da Deportibo da Balencia da Espanyol da Racing da kuma Osasuna.

Sauran solar hada da Billarreal da Almeria da Mallorca da Eibar da Atletico Madrid da Sporting da Tenerife da Hercules da Celta Bigo da Balladolid da Alabes da Lebante da Girona da Zaragoza da Las Palmas da Derez da Elche da Cordoba da Huesca da Leganes da kuma Cadiz.

What's On Your Mind?