Zamu Iya Lashe La liga –Simeone

- Advertisement -

Zamu Iya Lashe La liga –Simeone

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Atetico Madrid, Diego Simeone, ya bayyana cewa yana da kwarin gwiwar ‘yan wasansa za suyi iya yinsu domin lashe gasar cin kofin La liga na wannan kakar ake dab da karkarewa.

kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid, ta sake kama hanyar yiwuwar zama zakarar La liga a bana bayan shafe shekaru 7 ba tare da kai kofin gidanta ba, inda ta sake jan tazara tsakaninta da kungiyoyin Actual Madrid da Barcelona wadanda suka shafe shekaru suna lashe kofin.

Atletico bayan nasararta kan Actual Sociedad a ranar Laraba, yawan tazarar da ke tsakaninta da Barcelona wadda ke gurbin ta biyu a teburin gasar ya zama maki biyu, ya yinda ita kuma Barcelonar ke da tazarar maki biyu tsakaninta da Actual Madrid kuma Actual Madrid din ta samu nasara akan kungiyar Granada a ranar Alhamis.

Atletico Madrid dai na tunkarar kofin La liga na 11 ne a tarihi, kuma nasarar ta ta za ta tabbata ne idan har ta yi nasarar wasanninta biyu da suka rage kuma wasa na gaba da ke tunkaro kungiyar shi ne karawarta da Ossasuna a ranr Lahadi 16 ga watan Mayun da muke sai kuma karawarta da Actual Valladolid a ranar 18 ga wata.

 

- Advertisement -