Zamanin Kiwon Dabbobi A Sake Ya Shude – ACF

0
95

Zamanin Kiwon Dabbobi A Sake Ya Shude – ACF

Kungiyar Ta Goyi Bayan Matsayin Gwamnonin Arewa

A jiya Talata ne, Kungiyar Tuntuba ta Dattawan Arewacin Nijeriya (ACF) ta goyi bayan matsayin Kungiyar Gwamnonin Arewacin Nijeriya na cewar yin kiwon dabbobi a zamanance ya fi dacewa a halin yanzu, don haka ita ma take nanata cewa zamanain kiwon sake ya shude.

Sakataren yada labarai na sananniyar kungiyar na kasa Emmanuel Yawe ne ya bayyana hakan a cikin sanarwar da ya fitar a Jihar Kaduna.

Gwamnan Jihar Filato kuma shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewacin Nijeriya Simon Lalong ne ya bayyana matsayin gwamnonin a cikin  sanarwar da ya rabbata wa hannu  ya kuma fitar a ranar Litinin bayan  taron gaggawa  da kungiyar ta gudanar.

Fulani sun yarda ayi wa duk Makiyayi rajista, za su fallasa ‘Yan bindiga

A cewar kungiyar ta Arewacin Nijeriya, ci gaba da amfani da tsarin kiwon  sake a cikin bainar jama’a, ba zai ci gaba da dorewa ba idan aka yi la’akari da yadda al’umma ke kara karuwa a kasar nan da kuma bunkasar birane.

Kungiyar ta yanke shawarar ci gaba da ilimantarwa da kuma fadakar da Fulani Makiyaya kan bukatar su rungumi sabon tsarin kiwon dabbobi na zamani ta hanyar killace dabbobobi nasu a guri daya.

Kungiyar ta kuma yi kira da tattausar murya ga Gwamnatin Tarayya da ta taimaka wa jihohin da ke Arewacin kasar da kudade kai tsaye domin su fara awaitar ayyukan Ruga na zamani, musamman domin a wanzar da aikin kai tsaye

A cewar kungiyar, a wasu sasaan kasar nan ana ta suka kan yadda Fulani Makiyaya ke yin kiwo barkatai a bainar jama’a,  inda kuma haka ke janyo rikici a tsakanin musamman manoma da Fulani makiyaya har da rasa rayuka

Da yake karin bayani a sanarwar da kungiyar ta Dattawan Arewacin Nijeriya ta fitar, Sakataren yada labarai na kungiyar ta ACF  Yawe ya ce, “Muna goyon bayan gwamnonin Arewaci kan wannan matsayin nasu”.

What's On Your Mind?