Zaman Aure Shine Riba Amarya Sa’a Vocal – Jarumar Kannywood

0
101


Yanzu Yanzy An Fitar Da Katin Gaiyatar Daurin Auren Fitacciyar Mawaƙiya Kuma Marubuciya, Sa’adatu Isah Muhammad (Wadda Aka Fi Sani Da Laƙabin Sa’a Vocal) Ta Bayyana Cewa Aure Da Za Ta Yi A Ranar Lahadi Mai Zuwa Ba Zai Hana Ta Ci Gaba Da Rubutu Ba, Sai Ma Abin Da Ya Yi Gaba. 

Sa’a Vocal Ta Bayyana Hakan Ne Yayin Tattaunawar Ta Da Mujallar Fim Kan Batun Auren Ta Da Za A Ɗaura A Ranar 20 Ga Disamba, 2020.

Sa’a Matashiyar Marubuciyar Labaran Hikaya Na Zube Ce Kuma Sananniyar Mawaƙiya A Masana’antar Finafinan Hausa.

Haka Kuma Ma’aikaciya Ce A Gidan Talbijin Na Arewa24 Da Ke Kano.

‘yar Asalin Kano, Sa’a Vocal Ta Na Aikin Waƙa Ne Yawanci Tare Da Fitaccen Mawaƙi Naziru M. Ahmad (Sarkin Waƙa). 

Ɗimbin Waƙokin Da Ta Yi Tare Solar Haɗa Da ‘mai Waƙa’, ‘ba Zan Sake Ki Ba’, ‘mati Da Lado’ Da Kuma ‘mati A Zazzau’.

Haka Kuma Ta Yi Waƙa Da Nazifi Asnanic Mai Suna ‘ƙasar Mu Najeriya’, Da Dai Sauran Mawaƙa. 

A Ɓangaren Rubutu Kuma, Sa’a Vocal Ta Rubuta Littattafai Da Su Ka Haɗa Da ‘ƙauna Ce Sila’ Da ‘ƙaddarar Mu’. 

Mujallar Fim Ta Tambayi Mawaƙiyar Idan Angon Nata Shi Ma Mawaƙi Ne Ko Wani Jarumi A Kannywood, Sai Ta Amsa Da Cewa, “Ba Ɗaya; Ma’ana Ba Daga Cikin Mawaƙa Ya Ke Ba, Kuma Ba Daga Cikin Jarumai Ya Ke Ba.” Ta Ƙara Da Cewa, “Kawai Dai Allah Ne Ya Hukunta Hakan.” 

        Katin Gayyatar Auren Sa’a Vocal
A Kan Batun Yadda Zaman Aure Zai Shafi Rubutun Ta Da Sana’ar Ta Ta Waƙa, Amaryar Ta Bayyana Cewa, “Ko Bayan Yin Aure Na Ina Sa Ran Zan Ci Gaba Da Yin Ayyuka Na Na Rubututtuka, Wanda Kuma Ina Da Yaƙinin Cewa Rubutun Za Su Faɗaɗa Fiye Da Yadda Na Ke Yi Da. Waƙa Kuma A Yanzu Ba Zan Iya Cewa Komai A Kan Ta Ba.”

A Ƙarshe, Sa’a Vocal Ta Gode Wa Masoyan Ta, Marubuta, Mawaƙa, ‘yan Arewa24 Da Kuma Ogan Ta Naziru M. Ahmad.

Ta Kuma Buƙaci Masoyan Ta Da Su Taya Ta Da Addu’a, Ta Na Fatan Idan Solar Tuna Ta Za Su Yi Mata Addu’ar Dacewa A Duk Rayuwar Da Ta Tsinci Kan Ta.

Za Dai A Ɗaura Auren Sa’adatu Isah Da Angon Ta Haiwatu Sa’id Daud A Ranar Lahadi Da Misalin Ƙarfe 11:00 Na Secure A Masallacin Umar Bin Khaɗɗab Da Ke Shatale-talen Dangi Kusa Da Zoo Street, A Kano.

Allah Ya Kai Mu Kuma Ya Bada Zaman Lafiya Da Zuriya Ɗayyiba.

Kuyi Feedback Da Ra’ayoyin Ku.

What's On Your Mind?