Zaman Aure Bai Hanani Cigaba Da Yin Film – Rahama Sadau

0
46

Tauraruwar fina-finan Hausa,Rahama Sadau ta bayyana cewa yin aure ba zai sa ta daina sana’arta ta fim ba.

Ta bayyana hakane a matsayin amsa ga wani da ya tambayeta shin idan ta ti aure zata daina yin fim?

Rahama tace wane dalili zai sa ta daina yin fim? Tace akwai sana’o’i da ayyuka da dama da mata ke yi wanda basa dainawa idan solar yi aure, misali aikin jarida. Tace itama harkar Fim sana’a ce.

Rahama ta baiwa Masoyanta damar yi mata tambayoyine a shafinta na Twitter inda a nan ne ta bayar da wannan amsa.

Ta kuma bayyana cewa, yanzu haka tana soyayya da wani kuma har soyayyar ta yi karfi sosau.

Rahama ya kuma bayyana cewa itana tana so ta kawo wasu ta Raine su a masana’antar Kannywood kamar yanda Ali Nuhu ya mata.

wani yayiwa jarumar tambaya mi yafi bakanta mata rai akan Nigeria

Tace rashin tsaro.

 

 

What's On Your Mind?