Zaben Kananan Hukumomi: Sarkin Kano Ya Bukaci A Guji Tada Hankalin Al’umma

0
66

Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya bukaci Hukumar zabe mai zaman kanta (KANSEIC) da a tabbatar da ganin an gudanar da ingantaccen zabe tare da kaucewa duk wani abu da zai kai ga tada hankulan al’umma, domin dorewar zaman lafiya a Jihar Kano.

Alhaji Aminu Ado Bayero na wannan bayani ne alokacin da Hukumar gudanarwar KANSEIC ta ziyarce shi jiya Larabar a fadarsa cikin shirye-shiryen zaben Kananan Hukumomin Jihar na Kano.

Zaben Kananan Hukumomi: Sarkin Kano Ya Bukaci A Guji Tada Hankalin Al’umma

“An san Jihar Kano ce ke sahun gaba wajen zaman lafiya wanda ke zaman jagora ga sauran jihohin kasar nan, saboda haka sai ya jaddada bukatar cigaba da wayar da kan al’umma, domin gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali, musamman a lokacin gudanar daharkokin zaben tare da kaucewa duk wani abu da ka iya tada hankulan al’umma,” in ji Mai Martaba Sarkin.

Muhammadu Sambo Wali Gidadawa (Bagimbane): Gwarzonmu Na Mako (1)

Tunda farko a nasa jawabin, shugaban Hukumar zaben mai zaman kanta na Jihar Kano,  Farfesa Garba Ibrahim Sheka cewa ya yi, “mun zo wannan fada mai albarka ne domin neman sai albarka Sarki a shirye-shiryen zaben kananan Hukumomin Jihar Kano, kuma wannan fada ita ce matakin farko da muka fara tunkarar a wannan aiki.”

Farfesa Sheka ya shaidawa sarkin cewa, an tsaida ranar 16 ga Janairu, 2021, a matsayin ranar da za a gudanar da zaben bisa la’akari da dokar information hana nada kwntomomi kasancewar wa’adin mulkin wadanda ke kai zai kare a Fabrairu, 2021.

Wadanda ke cikin tawagar Hukumar photo voltaic hada da  sakataren Hukumar, Kwamishinonin Hukumar, daraktoci da sauran manyan jami’an Hukumar.

What's On Your Mind?