Zaben Kananan Hukumomi A Jihar Kaduna, Injiniya Ya Bai Wa Matasa Shawara

0
107

Zaben Kananan Hukumomi A Jihar Kaduna, Injiniya Ya Bai Wa Matasa Shawara

Zaben kanan hukumomi na Jihar Kaduna na kara kusantowa ‘yan takara na kara jan damara tare da neman goyan baya. karamanar Hukumar Sabon Gari Kowa ya san tana daya daga cikin kananan hukumomin da ke da matukar muhimmanci a bangaren sanin harkar siyasa a kasa baki daya.

karamar Hukumar Sabon Gari ta zama uwa a bangaren sanin kabli da ba’adin dake cikin siyasa a fadin jihar Kaduna da Arewacin Nijeriya. Bisa haka ne ake kallon duk wani dan siyasa da ya fito daga karamar Hukumar Sabon Gari to ya kan zama gago a ‘yan siyasa.
Bisa la’akari da hakan ne ya sa wakilinmu ya leka karamar hukumar don jin wace waina ake toyawa a halin yanzu musamman ganin yadda guguwar zaben ta fara kadawa a jihar.
Honorabul Muhammad Usman Injiniya, shi ne shugaban karamar hukumar Sabon Gari kuma daya daga cikin ‘yan takarar karamar hukumar a karkashin Jam’iyyar APC a karo na biyu a halin yanzu.
Shugaban tuni ya sayi Fom don kara neman damar komawa kujerar da yake kai a halin yanzu.
Bisa haka ne wakilinmu ya ji ta bakinsa a daidai lokacin da ya kammala jawabinsa taron kaddamar da shi a matsayin dan takarar shugaban karamar hukumar a karo na biyu ga dandazo jama’ar mazabar Bomo da ya gudana a unguwar Hayin Dogo dake samarun Zariya.
dan takarar kuma shugaban karamar hukumar daga farko ya nuna jin dadinsa ne bisa nuna kauna da bashi goyan baya da jama’ar karamar hukumar Sabon Gari suke yi a gida da waje.
Bayan haka ya yi matukkar godiya da bashi shawarar da aka yi na fitowarsa a karo na biyu don ci gaba da aikin alheri da ya faro ya ce, wasu an gama wasu yanzu aka fara ya yi fatan Allah ya sa hakan ya zame alheri ga jama’ar karamar hukumar.
Shugaban ya roki dukkan ‘ya’yan jambiyar APC da su zama masu tarbiyya a duk inda suke domin hakan shi ne siyasa ta kwarai.
Da shugaban ya juya kan matasa kuwa ya yi matukar kashedi ne a kan matasan da su kaucewa cin zarafin wani ko wasu a duk inda suke, yana cewa cin zarafin wani a siyasa ba abu ne mai kyau a rayuwa ba.
A halin yanzu tuni hotunan shugaban ya mamaye dukkan sako da lungu na karamar hukumar ta Sabon Gari wanda hakan na nuna cewa jama’a na kaunarsa.
Bincike ya nuna cewa hasken dan majalisar tarayyane ke kara fitowa da dan takarar kuma mutane na yi masa fatan alheri. Shugaban ya yi fatan Allah ya sa a yi zabe lafiya.

What's On Your Mind?