Za Mu Ruguza Gidajen Masu Yi Wa ‘Yan Bindiga Leken Asirin – Gwamnan Zamfara

0
102

Za Mu Ruguza Gidajen Masu Yi Wa ‘Yan Bindiga Leken Asirin – Gwamnan Zamfara

Mutane Da Dama Da Ke Birane Na Bai Wa ‘Yan Bindiga Bayanai

Daga Khalid Idris Doya,

Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Bello Matawalle, ya umarci jami’an tsaro da su gaggauta rushe gidajen masu leken asiri da masu yi wa ‘yan bindiga safarar makamai fadin jihar.

A wata sanarwar manema labarai mai dauke da sanya hannun Darakta Janar a fannin yada labarai na gwamnan, Malam Yusuf Idris, wanda kuma ya rabar wa ‘yan jarida a garin Gusau, ya bayyana cewar wannan umarnin ya fara aiki ne nan take ba tare da bata wani lokaci ba.

Matawalle ya bada wannan umarni mai zafin ne a lokacin da gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ya kawo masa ziyarar jaje dangane da harin baya-bayan nan da wasu ‘yan bindiga suka kai wasu kauyukan da ke cikin jihar na Zamfara, da hakan ya jawo mutuwar mutane da daman gaske da tursasa ma wasu yin hijira na dole.

Matawalle ya ce, daga cikin muhimman matakan da gwamnatinsa ta fara dauka kan wannan lamarin har da rushe dukkanin gidajen masu bada bayanai wa ‘yan bindiga da kuma masu sayo musu makamai tare da masu taimaka wa ‘yan bindigan da aka umarci a cafke su duk inda aka gano su.

Ya bayyana cewa daukan wannan matakin ya zama musu dole ne domin solar himmatu wajen ganin an tabbatar da dakile aikace-aikacen ‘yan bindiga da suka addabi wasu yankunan jihar.

A cewarsa, wasu mutane da dama na rayuwa cikin birane a boye amma suna samar da bayanai wa ‘yan bindigan da suke boye a cikin dazuka.

“Ayyukan ‘yan leken asiri (Informants) solar taimaka sosai wajen jawo matsaloli da daman gaske a kokarinmu na yaki da ‘yan bindigan a jihar,” ya lura kan cewa da cikakken hadin kai da goyon baya tabbas za a samu nasarar yakar ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga a fadin jihar.

 

Gwamnan ya kuma umarci sarakunan gargajiya da suke jihar da su kasance masu hakuri kana su maida hankali wajen bibiya da bin sahun dukkanin wadanda suka shigo cikin yankunansu domin tsame bata-gari daga cikin al’umma.

Ya bayyana cewar ta hakan ne jami’an tsaro za su samu taimakon bin diddigi da sawun duk wanda aka kai musu rahoto a kansa domin tabbatar da kare rayuka da dukiyar jama’a.

 

Tun da farko, Gwamna Aminu Tambuwal ya bayyana cewar ya zo Jihar Zamfara ne domin jajanta wa gwamnati da al’ummar jihar bisa kisan baya-bayan nan da ‘yan bindiga suka yi sakamakon hare-haren da suka kai wasu yankuna a jihar.

Ya misalta harin a matsayin na rashin imani, dabbanci da kidahumanci.

Gwamnan sai ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu a sakamakon wadannan hare-haren na ‘yan ta’adda.

Ya kuma jinjina wa Gwamna Matawalle bisa kokarin shawo kan dukkanin kalubalen tsaro da suke addabar jihar.

What's On Your Mind?