Zanga-zangar EndSARS: Za Mu Kare Dimukradiyyar Nijeriya – Janar Buratai

- Advertisement -

Za Mu Kare Dimukradiyyar Nijeriya – Janar Buratai

Babban Hafsan Askarawan Kasa na Sojojin Nijeriya, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai, ya fara murza gashin bakinsa, inda ya ja kunnen masu fakewa da zanga-zangar EndSARS su na aikata wa kasa da sauran ’yan Nijeriya ta’addanci, ya na mai kashedin cewa, shiru-shirun da dakarun sojojin kasar su ke yi, ba tsoro ba ne, inda ya ce, tabbas sojoji za su kare dimukradiyyar kasar a cikin kowane irin yanayi.

Janar Buratai ya bayyana hakan ne a wata sanarwa jiya mai dauke da sa hannun Darakta Mai Rikon Mukamin Jami’in Yada Labarai na Rundunar, Kanar Sagir Musa, jim kadan bayan ganawar janar din da kwamandoji da manyan jami’an bangarori daban-daban na rundunar.

Kanar Musa ya ce, bisa wannan dalili, Babban Hafsan Askarawan kasan ya umarci manyan jami’an da su daura damarar kare dimukradiyyar kasar, domin photo voltaic gano manufar wadanda su ke tunzura ’yan ta-more da sunan zanga-zangar, inda su ke fakewa da nagari daga cikinsu su na aikata muiyagun laifuka, don a taba su, in ya so su yi amfani da damar wajen bata sunan rundunar.

A ganawar, wacce a ka gudanar da ita a dakin taro na hedikwatar rundunar sojin kasa da ke Abuja, Buratai ya fito karara ya shaida wa manyan jami’an nasa cewa, kada su sake su yarda da rashin da’a ko biyayya a tsakanin jami’an soji, ya na mai umartar su da su tabbatar da kare dimukradiyyar Nijeriya ko ta halin kaka.

Janar Buratai ya ce, “tsarin gwamnati mafi kyau shi ne tsarin dimukradiyya. Don haka dole mu tabbatar da cewa, dimukradiyyar Nijeriya na tsaye da kafafunta kyam. Ba za mu bar wasu ’yan aike a ciki ko wajen kasar su tayar da zaune tsaye ba ga kasarmu ba.”

Ya cigaba da cewa, “abubuwan da su ka faru a ’yan kwanakin nan a kasarmu ta gado photo voltaic nuna yadda wasu batagari n mutane da kungiyoyi su ka dage kai da fata a kan lallai photo voltaic tayar da hankula a cikin kasar ko ta halin kaka.

“Wadannan mutane da tawagarsu photo voltaic gurbata zanga-zangar lumana ta EndSARS, inda su ka rikida ta zuwa tashin hankali da satar dukiyar al’umma a bangarori da dama na kasar, wanda hakan ya haifar da sanya dokar zirga-zirga a jihohi da dama na kasar,” in ji shi.

Janar Buratai ya kara da cewa, batagarin photo voltaic yi hakan ne, domin su kawo tunzuri, idan sojoji su ka dauki matakin kare al’umma, inda za su yi amfani da damar wajen ganin photo voltaic bata sunan rundunar da ma gwamnatin kasar.

“Ganin cewa, Rundunar Askarawan kasa ta na sane da wannan mugunyar shirin, sai ta ke yin taka-tsantsan, don kada a goga ma ta kashin kaji, amma ta tun a ranar 14 ga Oktoba, 2020, rundunar ta bayar da kashedi za ta kare dunkulalliyar Nijeriya.

“A yanzu kuma batagarin, tare da hadin bakin na cikin gida da waje, photo voltaic koma su na fakewa da tura sojoji da a ka yi a jihohin da a ka sanya dokar zirga-zirga, wacce halastattun hukumomi su ka kafa a jihohinsu, don tabbatar da dokar, musamman a Jihar Legas da sauransu.

“Masu fafariton su na yi wa rundunar kojojin kasa kazafi, duk da cewa, akwai shaidu karara da su ka saba da hakan. Photo voltaic cigaba da yin barazanar gurfanar da Rundunar Kasa a gaban Kotun Duniya (ICC) da kuma yin barazana daban-daban ga jami’ai da iyalinsu.

“Amma alhamdulillahi, mafi yawan ’yan Nijeriya da kungiyoyin kasashen duniya photo voltaic gano ’yar burum-burum din da makiyan Nijeriya ke yi,” in ji sanarwar.

Buratai ya ce, “duk da hakan, Rundunar Askarawan Kasan Nijeriya ta cigaba da yin taka-tsantsan ta hanyar bin ka’idojin dokokin cikin gida da na waje, wadanda a ka tsamo su daga dokokin kula da hakkin bil adama gwargwadon ka’idojin yin amfani da karfin tuwo.”

Sai dai ya kara da yin amfani da wannan dama wajen jan hankalin mahalarta ganawar da kada su ji tsoron yin barazana da Kotun Duniya wajen hana su aiwatar da halastaccen aikin da Kundin Tsarin Mulkin Kasa na 1999 ya dora mu su (wanda a ka gyara) da sauran dokokin Nijeriya.

Ya ce, “sojoji su na da dama a Kundin Tasrin Mulki su aiwatar da aikinsu na tabbatar da doka da oda ta hanyar tallafa wa hukumomin farar hula da sauran jami’an tsaro.

“Don haka duk mai shakkun kan aikinsu na sauke nauyin da a ka dora mu su, dole ne ya san cewa, sojoji a shirye su ke da su tabbatar da zaman lafiya, hadin kai da tsaron Nijeriya.”

Sai ya ja hankalin sojojin Nijeriya da su nuna wa batagari cewa, ba za su iya hana sojoji aiwatar da aikin da Kundin Tsarin Mulki ya dora mu su ba, ya na mai cewa, a dauki matakin kan duk wani mataki da wani ya dauka na halaka sojoji, jami’an tsaro da sauran ’yan kasa masu bin doka nan take.

Janar Buratai ya kara da cewa, “a yayin maganta matsalar tsaron, sojoji su tabbatar su na yin cikakken hadin gwiwa da jami’an Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya da sauran jami’an tsaro, don tabbatar da cewa, kowa ya bi umarnin dokar hana zirga-zirga da a ka kafa.”

Daga nan sai ya bayyana cewa, ayyukan batagarin ya nuna yadda su ke kokarin mallakar makamai da alburusai ko ta halin kaka daga hannun jami’an tsaro. Kimanin bindigogi kirar AK-47 guda 10 a ka rasa a hannun batagarin cikin makonni biyu a fadin kasar, baya ga rasa rayukan jami’ai da a ka yi.

Don haka sai ya umarci manyan kwamandojin da su tabbatar da sa ido tare da umartar jami’ansu da su ankara da halin da a ke ciki a cikin barikinsu da wajensu a koyaushe.

A karshe Janar Buratai ya ce, “babu wani zabi bayan tabbatar da dimukradiyya a dunkule tare da Nijeriya mai yalwar arziki.”

Daga nan sai kwamandojin da shugabannin sassan tsaron su ka sake daukar alkawarin kare Nijeriya, hadin kanta da zababbiyar dimukradiyyarta ko ta halin kaka ba tare da jin tsoro ba.

- Advertisement -