Za Mu Dauki Tsattsauran Mataki Kan Dokar Hana Sukuwar Dawakai – Gwamnatin Neja

- Advertisement -

Za Mu Dauki Tsattsauran Mataki Kan Dokar Hana Sukuwar Dawakai – Gwamnatin Neja

Daga Muhammad Awwal Umar, Minna

 

 

A cikin satin da ya kare ne gwamnatin Neja ta fitar da sanarwar hana sukuwar dawakai a dukkanin masarautun jihar, inda ta nuna cewar za ta dauki tsattsauran mataki ga dukkan wanda ya saba wa dokar.

Sanarwar da ta fito daga ofishin sakataren gwamnatin jihar wanda jami’in yada labaran ofishin Malam Lawal Tanko ya sanya wa hannu ta bayyana haka.

Da yake karin haske ga manema labarai, Malam Lawal Tanko ya ce bisa kiraye-kirayen jama’a da korafe-korafen da gwamnati ke samu kan yadda mahaya dawakai suka mayar da abin al’ada da idan ana bukukuwa matasa kan dauko dawakai ana sukuwa a cikin unguwanni hakan kan zama barazana ga lafiyar al’umma, “don haka gwamnatin jiha ta soke shi gaba daya, kuma gwamnatin ta dauki matakin hana duk wani abu da zai iya zama barazana ga zaman lafiya ko tada hankulan jama’a duba da irin halin da jihar ke ciki yanzu, saboda haka haramcin bai tsaya kan bukukuwan sallah ba kadai, ya shafi dukkanin wani bukin da ake shiryawa na aure ko akasin sa. Duk wanda ya saba wa dokar aka kama shi ya tabbatar da zai fuskanci fushin gwamnati domin gwamnati ba za ta bar jama’a kara zube kowa na aiwatar da abinda ya ga dama ba tare da la’akari da hadarin da zai jefa al’umma ba.” In ji sanarwar.

Takardar sanarwar ba ta tsaya nan ba, ta kuma yi karin haske a kan masu rubuce-rubucen batanci da karairayi a yanar gizo, inda sakataren gwamnatin, Ibrahim Musa Matane ya bayyana cewar daga yanzu duk wani da aka samu da rubutun batanci ko cin zarafin wani a yanar gizo gwamnati a shirye take wajen daukar mataki a kanshi.

Takardar ta ce akwai wadanda suka dauki dabi’ar shiga yanar gizo dan kaga abubuwan da suka ga dama ba tare da la’akari da illar da hakan zai janyo ba, saboda haka gwamnati ta soke irin wadannan dabi’un, a halin da jihar da kasa ke ciki tana neman hadin kan al’umma da yin addu’o’in samun zaman lafiya ne ba takalo abubuwan da za su cigaba da janyo baraka ba.

Gwamnatin jiha, bisa jagorancin Alhaji Abubakar Sani Bello ta dauki kwakkwaran matakai na kare rayuka da dukiyoyin jama’a, duk wani abinda zai zama kafa na rashin zaman lafiya gwamnatin a shirye ta ke wajen kawar da shi.

- Advertisement -