Za Mu Cigaba Da Tallafa Wa Mata Da Kayan Sana’o’i, Cewar Matar Gwamnan Bauchi

0
45

Matar gwamnan jihar Bauchi Hajiya Aisha Bala Muhammad ta shaida cewar za ta ci gaba da kokarin samar wa iyaye mata tallafi da kayayyakin koyon sana’o’in domin su ma su tsayu da kafafunsu ta fuskacin sana’o’in hannu don kyautata rayuwarsu da na iyalansu a kowani lokaci.

Hajiya Aisha Bala ta shaida hakan ne a jiya sa’ilin da take kaddamar da shirin rabon tallafin kayayyakin sana’o’in hannu wa iyaye mata 100 a karamar hukumar Toro wacce ofishinta da hadin gwiwar ofishin kwamishinar mata na jihar suka dauki nauyin rabawa ga matan da suke bukatar hakan kyauta domin agaza wa rayuwarsu.

Ta ci gaba da cewa tun lokacin da ta samu kanta a matsayin matar gwamnan jihar take kan kokarin tallafa wa iyaye mata da ‘yan mata a sassa daban-daban na jihar wacce kawo yanzu mata da sama suka ci gajiyar tallafin nata, a cewarta ba su jari da tallafin kayan gudanar da sana’o’i na daga cikin hanyoyin da take bi wajen kyautata rayuwar mata a fadin jihar.

Ta kara da cewa tana yin irin wannan ne domin saka wa irin gudunmawa da mata suka bayar wajen samun nasarar mijinta, sai ta sha alwashin ci-gaba da samar da ababen further rayuwa ga mata da ‘yan mata a fadin jihar.

Tun da farko, Kwamishinan mata da cigaban yara ta jihar Bauchi Hajiya Hajara Jibrin Gidado ta shaida cewar wannan tallafin kayan sana’o’in zai yi matukar taimaka ma wadanda suka ci gajiyarsa ta fuskacin saukaka musu wahalhalun rayuwa na yau da gobe.

Za Mu Cigaba Da Tallafa Wa Mata Da Kayan Sana’o’i, Cewar Matar Gwamnan Bauchi

Ta shaida cewar za su karade dukkanin kananan hukumomin jihar wajen yin irin wannan rabon kayan tallafin, inda ta ce nan da ‘yan kwanaki za su isa wasu kananan hukumomin bayan kaddamar da shirin a garin Toro.

Hon. Gidado ta nemi ‘yan uwanta mata da su ci gaba da mara wa gwamnati mai ci baya domin ta samu nasarar kyautata rayuwar al’ummar jihar a kowani lokaci.

Ta na mai cewa tun lokacin da suka zo kan mulki ofishinta da na Matar gwamnan suke kan fito da tsare-tsare na ganin rayuwar mata da yara ya samu ingantuwa a jihar Bauchi.

Kwamishinar ta gargadi matan da suka samu tallafin da cewa kada su yi gigin saida kayayyakin da suka samu tallafin kana kada su daura wa ‘ya’yansu tallah, ta nemi matan da cewa suke gudanar da ‘yan kananan sana’o’in su a cikin gida domin rufa wa rayuwarsu asiri.

UNIBEN Extends Post-UTME registration for 2020/2021 academic session

“Idan kuka nutsu kuka sarrafa wadannan kayan da kuka samu ta hanyoyin da suka dace zai yi matukar taimaka wa tattalin arzikinku. Sannan, muna son ku aiwatar da sana’o’inku a cikin gida domin muna kan fadakar da jama’a cewa su guje wa daura wa yaransu tallah, ba sai kun tura ‘ya’yanku tallah kafin ku samu ciniki ba, a cikin gida za ku iya samun kwastomomi muddin aka maida hankali kan sana’o’in da ake yi.”

Ta ce kananan hukumomi da dama ne suka amfana da irin wannan tallafin kayan sana’o’i na miliyoyin naira daga matar gwamnan da hadin guiwar oshinta sai ta gode mata a bisa irin wannan kokarin nata.

Malama Asmau Muhammad tana daga cikin wadanda suka samu cin gajiyar shirin, ta gode wa Matar gwamnan da kwamishinan mata na jihar a bisa wannan tallafin nasu a garesu. Matan photo voltaic yi alkawarin amfani da kayan da suka samu ta hanyoyin da suka dace domin kyautata rayuwarsu da na iyalansu.

An tallafa wa matan da nau’ukan kayan gudanar da sana’o’in hannu na mata daban-daban wadanda kowacce mace ta zabi sana’ar da ta ke yi ko za ta yi, domin karfafa mu su gwiwa.

What's On Your Mind?