Za A Yi Taron Kaddamar Da Littafin Diwanin Wakoki Na Aminu Ladan Abubakar Ala

0
176

Za A Yi Taron Kaddamar Da Littafin Diwanin Wakoki Na Aminu Ladan Abubakar Ala

Daga Mukhtar Yakubu a Kano

karo na farko a kasar Hausa an samar da wani babban littafi wanda ya ke kunshe da tarihi da kuma wakokin Mawakin Hausa na zamani.

Littafin mai suna DIWANIN WAKOKIN AMINU ALA. Ya kunshi tarihin rayuwarsa tun tasowar sa da asalin sa da yadda ya fara waka da kuma wasu ayyukan da ya gudanar a rayuwar sa zuwa yanzu.
Domin jin ta bakin sa dangane da samuwar littafin. Wakilin mu ya tattauna da (Dakta) Aminu Ladan Abubakar Ala in da ya bayyana mana muhimancin littafin a wajen in da muka fara da tambayar sa yadda ma rubutun littafin ya kasance kamar yadda muka ji daga bakin sa cewar
“To wannan Diwani an fara shirin rubutun sa tsawon shekaru biyar ko shida da suka wuce, kuma a yanzu ya kai ga gabar kammaluwa saboda a yanzu muna shirye shirye ne da ‘yan kwamiti na yadda za a kaddamar da shi a bayan Sallah, don haka abin da kwamitin suka zartar da rana da kuma lokaci da garin in sha Allahu za a yi taron kaddamar da shi.

Kuma littafi ne da Marubuta biyu suka yi hadaka wajen rubuta shi wato Farfesa Salisu Ahmad Yakasai,na Jami’ar Danfodiyo da Abu Ubaida wanda shi ma Dalibi ne a Jami’ar Danfodiyo.

Duk da ya ke ba kai ka rubuta ba Amma kamar yadda ka fada an shafe wajen shekaru shida ana aikin rubutun don haka ba za ka rasa masaniya ba wajen yadda aikin littafin ya gudana.

To wannan dai na san tun da abu ne da ya fito daga Jami’ar Danfodiyo, kuma musamman shi Farfesa Salisu Ahmad Yakasai fitaccen Malami ne wanda a yanzu shi ne shugaban sahin fassara, kuma marubuci ne ya rubuta littattafai da dama da suka shafi ilimi da dama a Fannin rayuwa daban daban to ka ga kuwa tun da masana ne suka yi abin to za su yi shi ne tun daga tushe, amma dai ta ta bangare na na san an tambaye ni wasu abubuwa wanda in ba a waje na ba, to ba za a identical su ba, kamar misali ka ga akwai hotuna da suka bayyana na cikin gida tare da iyalaina da kuma wasu daga cikin ‘yan uwa na da ahakikai na wanda iya iya rayuwata za ka ga ba a ganin hoton iyalaina, ba a san’ ya’yana ba ma saboda haka hotunan yara na da suka bayyana a duniya ba su fi biyu ba kuma su ma ‘yan kanana. To Amma ka ga wannan da ya ke bincike ne na masu ilimi an samu komai har da hotuna na tun ina harkar kwallon kafa, ina za a samu wannan in ba a waje na ba. To sannan kuma akwai sauran hanyoyin bincike irin na su da su ke bi na masana, kamar binciken wasu abubuwan da aka yi a baya, tun da akwai littafi da Muhammad Lawan Barista ya yi a kan wakokina, sai kuma wanda muka rubuta ni da Auwalu Danbarno mai suna Alfanda Amadu, wanda muka yi a kan tarihin Ahmadu Sardauna, sannan kuma akwai littafi da na yi na shahara, kuma dai akwai hanyoyin bincike irin na su na masana.
Ko me ya bambanta wannan littafin da sauran wadanda aka rubuta a baya?
To ai tun daga sunan ma ya Bambanta sannan kuma daga Alkalamin mai rubutun, wannan Farfesa Salisu Ahmad Yakasai mun dade da shi kamar yadda muka dade da Muhammad Lawan Barista, shi aboki na ne, wannan kuma Malami na ne, kuma shi wannan an yi masa take da Diwani, kuma yawan shafukan sa ya zarce na baya, don wannan ya kai shafi wajen 628, to na baya bai Kai haka ba don haka akwai bambanci sosai a tsakanin su.

Wannan wata baiwa ce da Allah ya ba kaa fagen waka da har aka kai ga yin wannan Babban littafi a kan ka wanda kai ne Mawakin zamani na farko da aka yi irin wannan aikin a kan sa ya ka kalli wannan matsayi da Allah ya ba ka?
Gaskiya na ga wani rubutu ma an hada da hoto na yana yawo cewar shi ne farkon kaza daga kan sa aka fara yin kaza. To wannan tambayar ta ka sai ta Kara tuna mini da wancan rubutun don gaskiya a cikin mawakan zamani na wannan lokacin, a kaina aka fara rubuta Diwani a kan mawaki kuma ya fito daga sashin harsuna na kasa daga Jami’a wani babban Malami Farfesa ya yi rubutu a kan mawaki na zamani ni ne na farko, wannan abin godiya ne kuma aka yi rubutun da Mafi yawan masu Adabi ba sa dacewa da ana tattara abubuwan da suka yi sai bayan solar mutu.

Don yawancin masu Adabi suna ganin cewar duk abin da ka rubuta to akwai saura a gaba, tun da bai mutu ba zai iya zuwa da wani abu wanda kai ba ka zo da shi ba, to wasu suna tattara bayanan mutum ne idan ba shi da rai, to Amma wannan sai aka yi sa’a ga shi an samu tarin ayyukan baya kamar yadda shi Farfesa ya ke cewa solar mayar da hankali wajen ayyukan baya ne saboda kada su wuce ba a taskace su ba, amma dai ya ce ba tsayawa za su yi ba za su ci gaba ne, wannan dalilin ne ma ya sa mu ke so a kaddamar da littafin saboda abin da aka kashe ya dawo, don a sabunta a ci gaba da yin aikin na gaba saboda wannan bugu na daya ne akwai na biyu kuma za a ci gaba da yin sa har illa masha Allah. Don haka na godewa Allah ina kuma alfahari da hakan. Dama ce da Allah ya ba ni har ya nufa za a yi, saboda ni babu ko sisi na a cikin aikin, ba a nemi tallafin komai daga waje na ba in ban da tambayoyi da bayanai kamar yadda Dalibai su ke yi mini, don haka babu kudi na a ciki, ka ga wannan abin alfahari ne a gare ni da aka yi mini abu don Allah da kuma cantanta ta.

Dangane da maganar kaddamarwa da ka ce ana kan aikin ta a yanzu a wacce gaba a ke?
To ana kan shiri a yanzu domin kuwa taro ne da za a yi shi Wanda ba za mu kira shi da karamin taro ba, don zai zama shi ne taro na farko da za mu shirya gagarumi, saboda haka muna son mu yi Babban taro na masoya, duk in da masoyi ya ke muna bukatar ya zo ranar da za a kaddamar da wannan littafi wanda ya ke dauke da tarihi na da nasaba ta bangaren uwa da bangaren Uba, da tarihin kuruciya ta da tasowa ta da wakoki na da ma wasu abubuwa da ba a sani ba, don haka wannan babban taro mu ke so mu yi wanda za mu kaddamar da wannan littafin don a samu kudin da za a ci gaba da yin aikin, don haka a yanzu gabar da mu ke ciki muna tattaunawa da kungiyar Masoya Ala wanda shi ma kan sa Farfesa Salisu Allah Yakasai yana cikin ta, kuma muna son mu miki komai a wajen kungiyar ta masoya Ala don ta tsara ta kuma gudanar da taron, don haka su ne za su gayyato duk wani masoyi da ya ke da sha’awar Adabi da kuma muhimman mutane wanda su ma solar san wannan abin aikin al’umma ne, misali akwai masu kudi da shugabanni da Malamai, to in dai za a yi wannan taron za ga dukkan bangarori na jama’a a wajen.

Menene sakon ka na karshe?
Sako na dai shi ne mutane su sani wannan al’amari dai gagarumi ne in sha Allahu duk wanda ya ga katin gayyata bai je masa ba, to sai dai mun manta ne ko kuma bisa kuskure, amma dai muna bukatar duk wani mahaluki a wajen wannan taron don za mu gayyato Marubuta, manazarta, Malaman Addini da sarakuna iyayen al’umma, don haka taro ne da mu ke sa ran zai zama zakaran gwajin dafi, muna fatan dai Allah ya ba mu sa’ar yin taron mu kuma cimma manufar da ta sa muka shirya shi. Nagode Allah ya ba mu sa’a.

What's On Your Mind?