Za A Samar Da Kasuwar Wiwi Mafi Girma A Duniya

0
134


A wani Rahotanni solar bayyana cewa majalisar dattawa a Mexico, ta amince da wata doka da ake sa ran za ta bayar da dama domin samar da kasuwar sayar da wiwi mafi girma a duniya.
Idan Majalisar Wakilan ƙasar ta bayar da goyon baya kan hakan, haka kuma idan ta amince da shan wiwi domin nishaɗi, za a rinƙa amfani da tabar wiwin wurin binciken kimiyya da kuma haɗa magunguna da kuma sarrafa tabar a kamfanoni.

Wannan kudurin na zuwa ne a daidai lokacin da Mexico ke ƙoƙarin yaƙar manyan dillalan miyagun ƙwayoyi a ƙasar.

What's On Your Mind?