Za A Iya Cim Ma Burin Wadata Nijeriya Da Abinci Ne Kawai In An Gudanar Da Dimbin Ayyuka A Fanni –Dakta Hyde

- Advertisement -

Za A Iya Cim Ma Burin Wadata Nijeriya Da Abinci Ne Kawai In An Gudanar Da Dimbin Ayyuka A Fanni –Dakta Hyde

Daga Abubakar Abba,

Shugaban Cibiyar baje kolin Kasuwanci da masana’antu da ke a garin Fatakwal Dakta Hyde  Ochia ya yi kira da a gudanar da ayyuka masu dimbin yawa, musamman don a cimma bukatar da ake da ita a kasar nan, wajen wadata kasar da wadataccen abinci da kuma cimma burin tsarin habaka noma a Nijeriya.

Ya sanar da hakan ne a hirarsa da manema labarai a garin Fatakwal a ranar litinin information gabata, inda ya yi nuni da cewa, Masana’antun dake sarrafa abinci a cikin kasar nan, zasu iya taimakawa wajen bunkasa tattalin arzinkn Nijeriya  da samar da  sababbin dimbin ayyukan yi ga yan kasar nan, in har an basu  goyon bayan da ya dace.

Shugaban Cibiyar baje kolin Kasuwanci da masana’an na garin Fatakwal Dakta Hyde  Ochia ya ce,  babbar hanyar bunkasa samar da abinci, kunshe take da samun hauhawan farashi da goyon bayan da masana’anta take samu da gudanar da ayyukan ta na yau da kullum da kuma kara habaka samar da ayyukan yi ga jama’a.

A cewar Shugaban Cibiyar baje kolin Kasuwanci da masana’an na garin Fatakwal Dakta Hyde  Ochia, sarrafa abinci ya kara samun tagomashi, idan akayi la’akari da  karin samun ayyukan da aka daukaka ta hanyar   habaka ajandar farfado da aikin noma (ATA).

Shugaban Cibiyar baje kolin Kasuwanci da masana’an na garin Fatakwal Dakta Hyde  Ochia, inda ya ci gaba da cewa, kara samun sarrafa abinci a kasar nan, ya kuma tabbatar da  raguwar karin nauyi akan shirye-shiryen samar da ayyukan yi a kasar nan.

A cewar Shugaban Cibiyar baje kolin Kasuwanci da masana’an na garin Fatakwal Dakta Hyde  Ochia, masana’antun sarrafa abinci  dake cikin  kasar nan,  kai tsaye zasu taimakawa   ciyar da fannin aikin noma da kuma rayuwar manoman dake cikin kasar nan.

Ya yi nuni da cewa, masana’antun dake sarrafa abinci a cikin kasar nan, suna fuskantar matsalar wutar lantarki, inda hakan yake shafar ayyukan da auke gudanarwa na yau da kullum.

Shugaban Cibiyar baje kolin Kasuwanci da masana’an na garin Fatakwal Dakta Hyde  Ochia ya kara da cewa, karancin na wutar lantarki, na dakile ciyar da masana’antun na sarrafa abinci gaba.

Da yake yin tsokaci kan abinda ke kara dakushe ayyukan masana’antun na sarrafa abinci a cikin kasar nan,   Shugaban Cibiyar baje kolin Kasuwanci da masana’an na garin Fatakwal Dakta Hyde  Ochia ya ce, akwai bukatar a rage daukar tsauraran matakai  akansu.

Ochia ya kuma yi nuni da cewa, masana’antun na sarrafa abinci daka kasar nan, suna taimakawa wajen samar da mafita ga bukatar.da ake da ita ta abinci  da kiwon lafiya da kuma habaka tattalin arziki.

Shugaban Cibiyar baje kolin Kasuwanci da masana’an na garin Fatakwal Dakta Hyde  Ochia ya numa yi nuni da cewa, idsna akayi la’akari da irin dimbin jarin da aka zuba a fannin aikin noma  a daukacin fadin kassr nan, ya ce akwai bukatar a habaka fannin na sarrafa abinci a kasar, musamman don a rage tabka asara.

A cewar Shugaban Cibiyar baje kolin Kasuwanci da masana’an na garin Fatakwal Dakta Hyde  Ochia da akwai dimbin dama da ake sama a fannin na sarrafa abinci a kasar nan.

Shugaban Cibiyar baje kolin Kasuwanci da masana’an na garin Fatakwal Dakta Hyde  Ochia ya kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya information    samar da kyakyawan yanayin da ya dace ta hanyar samar da tsare-tsare da bin ka’idoji a tsakanin masana’antun sarrafa abinci masu zaman kansu dake a daukacin fadin kasar nan.

- Advertisement -