Za A Gudanar Da Baje Kolin Hajojin Sayayya Irin Sa Na Farko A Haikou

- Advertisement -

Za A Gudanar Da Baje Kolin Hajojin Sayayya Irin Sa Na Farko A Haikou

Daga  CRI Hausa

Kasar Sin ta shirya gudanar da bikin baje kolin kasa da kasa, na hajojin sayayya irin sa na farko a birnin Haikou, fadar mulkin lardin Hainan, tsakanin ranekun 7 zuwa 10 ga watan Mayun nan.

Baje kolin zai kasance na farko da za a gudanar a Hainan, tun bayan da a watan Yunin bara, Sin ta fitar da babban shirin ta na mayar da tsibirin na Hainan, kasaitaccen lardi da zai zamo cibiyar kasa da kasa mai tasirin cinikayya, kuma tashar ruwa ta cinikayya cikin ‘yanci nan da tsakiyar wannan karni.

Kaza lika baje kolin zai zamo irin sa na farko, da zai maida hankali ga hajojin sayayya, wanda kasa ta biyu a karfin tattalin arziki a duniya za ta gudanar.

Ana sa ran wannan baje koli zai fayyace karfin sayayyar al’ummar kasar Sin, tare da ingiza ginin ababen extra rayuwa da ake bukata, a tashar ruwa ta cinikayya cikin ‘yanci, kana zai zama wata dama ta samun ci gaban tattalin arziki ta hanyar cudanya a kasuwannin cikin gida da na ketare. (Mai fassarawa: Saminu daga CRI Hausa)

- Advertisement -