Yunkurin Tsaida Nijeriya Cak! Kungiyar Gwamnoni Ta Nemi NLC Ta Janye Batun Yajin Aiki

0
75

Kungiyar Gwamnonin Nijeriya da kungiyar kwadago ta kasa NLC photo voltaic kama hanyar warware matsalolin da ya kai ga ayyana shiga yajin aiki daga gobe Litinin a fadin kasar nan na cewa, sai gamnati ta janye karin farashin kudn mai dana wutar lantarki da ta kara kwanakin baya a fadin kasar nan, ana kuma sa ran yajin aikin zai tsayar da harkokin yau da kullum a Nijeriya cak!.

Sanarwa da ta fito daga ofishin watsa labarai na kungiyar gwamnanonin ya nuna cewa, sakamakon ganawar da aka yi tsakanin shugabanin kungiyar kwadago a wanda da aka yi a gidan shugaban kungiyar gwmananonin da ke Abuja ranar Asabar, ya nuna lallai a kwai fahintar juna a tsakanin bangarorin biyu.

Shugaban kungiyar gwamnanonin kuma Gwamnan jihar Ekiti, Dr John Kayode Fayemi ya jagoranci bangaren gwamnonin yayin da shugaban kungiyar kwadago, Kwamrade Ayuba Wabba tare da rakiyar shugaban TUC, kuadri Olaleye da kuma sakataren kungiyar Emmanuel Ugboajah, suka jagoranci bangaren kungiyar kwadagon, haka kuma darakta janar na kungiyar gwamnonin, Mr Asishana Okauru shi ma ya samu halartar taron.

Shugaban kungiyar gwamnonin ya ce, kungiyar gwamnonin photo voltaic yanke hukuncin shiga lamarin ne don samar da yanayin da za a tattauanwa don a kaucewa shiga yajin aikin da ake shirin fadawa.
Ya kuma roki ‘yan kwadagin kan cewa, shiga yajin aiki a wannan lokacin zai kara jefa al’umma cikin halin mi ‘ya su da suke ciki na wahalar rayuwa.

Fayemi ya ce, halin da ma’aikata suke ciki ya riga ya munana kuma shiga wani yajin aiki zai kara jefa al’umma cikin mummunan hali ne.

Yunkurin Tsaida Nijeriya Cak! Kungiyar Gwamnoni Ta Nemi NLC Ta Janye Batun Yajin Aiki

Shugaban kungiyar gwamnonin ya kuma ce, babu wani a kasar nan da ba zai yarda da bayanin ‘yan kwadago ba na halin da ma’aikata suke ciki, amma lallai ya kamata kungiyar ta sake duba lamarin shiga yajin akin.

Gwamnonin photo voltaic kuma bukaci a basu lokaci na tattaunawa da bangaren sakataren gwamnatin tarayya da kuma ofishin mataimakin shugaban kasa don samar da mafita.

Ya kuma yi alkawarin ba lamarin mahimmaci, kuma da zaran ya tashi daga wannan tarin zai zarce ne fadar shugaban kasa don ganawa da su a kan lamarin.
Shugabann kingiyar gwmanonin ya kuma ce yana fata wannan kokarin na su zai taimaka wa kungiyar kawdagon na janye yajin aikin da suke shiryawa.

A bangaren sa, shugaban kungya kwadagon ya ce, gwamnatin tarayya ta karya dukkan yarjejeniyar da suka yi da kungiyar, ya kuma godewa shugaban kungugiyar gwmanonin a kan yadda suka shiga lamarin.

Da zaran an kara kudin man fetur kusan farashin komai yana tashi ne, in ji shugaban kungiyar kwadagon.

Ya amince da shugaban kungiyar kwamnonin ya kuma gode masa akan kokarin fadada tattauanwa akan lamarin

What's On Your Mind?