Yobe Za Ta Fadada Zangon Tashar Yada Labaranta  

- Advertisement -

Yobe Za Ta Fadada Zangon Tashar Yada Labaranta  

Daga Muhammad Maitela,

Kwamishina a ma’aikatar yada labarai, al’adu da harkokin yau da kullum a jihar Yobe, Hon. Abdullahi Bego ya bayyana kudurin gwamnatin jihar, karkashin Gwamna Mai Mala Buni wajen fadada zangon tashoshin yada labaran jihar don samun nasarar fadakar da al’umma dangane da ayyukan ci gaba da gwamnati ke gudanarwa tare da sadar da jihar da sauran bangarorin duniya.

 

“Saboda a lokaci irin wannan, biyo bayan matsalar tsaron da al’ummar jihar Yobe suka sha fama dashi, wanda hakan zai taimaka wajen ci gaba da fadakar da jama’a, ilmantarwa da nishadantar dasu dangane da muhimmancin zaman lafiya da mu’amala da juna, wanda gwamnatin jihar Yobe ta ga akwai bukatar sake bunkasa/ fadada tashoshin ta na yada labarai, musamman gidan rediyon ‘Yobe Broadcasting Company’ (YBC), domin shiga lungu da sakon jihar.”

 

Alhaji Abdullahi Bego, ya bayyana hakan a wani shirin tattaunawa da kwamishinoni a jihar dangane nasarorin da ma’aikatunsu suka cimma, a daidai lokacin da Gwamna Buni ke cika shekaru biyu a karagar mulkin jihar, wanda ya gudana a Sakatariyar uwar kungiyar NUJ a Damaturu, wanda aka yi wa take da: ‘bunkasa ci gaba tare da shugabanci nagari’.

 

Bugu da kari kuma, Kwamishina Bego ya yi karin haske da cewa a halin yanzu zangon tashar gidan rediyon jihar bai wuce yankin Dapchi ba, wanda ya shaidar da cewa gwamnatin jihar za ta dauki matakin fadada zangon zuwa baki dayan kananan hukumomin arewacin jihar, wadanda suka hada da Machina, Nguru, Karasuwa, Yunusari, Yusufari da Geidam.

 

A hannu guda kuma, Bego ya nusar da cewa Gwamna Mai Mala Buni ya bayar da umurnin sayo sabbin kayan aikin da suka dace ayi amfani dasu ta wannan bangaren, “wadanda za a sanya su a karshen wannan shekara. Sannan kuma zan yi amfani da wannan dama wajen bayyana wa Gwamna Buni godiya tare da yaba wa namijin kokarinsa wajen ci gaba da bai wa ma’aikatar yada labarai ta jihar Yobe cikakken goyon baya domin samun tabbacin cimma muradun da ta sanya a gaba a kokarinta na fadakar da al’ummar jihar Yobe da sahihan bayanan da suka dace.”

 

- Advertisement -