Yobe Ta Dauki Sabbin Matakan Takaita Mutuwar Kananan Yara A Jihar

- Advertisement -

Yobe Ta Dauki Sabbin Matakan Takaita Mutuwar Kananan Yara A Jihar

Daga Muhammad Maitela, Damaturu

A kokarinta wajen takaita mutuwar kananan yara da rage wahalhalun da masu juna biyu ke fuskanta a yankunan karkara, gwamnatin jihar Yobe ta dauki matakan shawo kan wadannan matsaloli ta hanyar daukar sabbin matakai wadanda suka hada da ware sama da naira miliyan 179 domin sayo karin wasu kekuna 60 masu taya uku na musamman domin jigilar majinyata (Tricycle Ambulance) zuwa asibitoci mafi kusa dasu, a sassan jihar.

Kwamishina a ma’aikatar kiwon lafiya ta jihar Yobe, Dr Mohammed Lawan Gana shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a sakatariyar NUJ dake babban birnin jihar a Damaturu ranar Laraba tare da bayyana cewa ma’aikatar tana iya kokari wajen aiwatar da daukar matakan kariya daga annobar korona.

Ya ce, “Wanda domin ganin samun tabbacin kayan aikin suna gudana ba tare da wata tangarda ba, a bangaren gwamnatin da masu zaman kansu, mun sanya ido sosai ta hanyar kafa kwamitin kwararru wanda zai sanya ido tare da kula domin ganin al’amurra suna gudana kamar yadda aka tsara.”

“Har wala yau, kawowa yanzu kwalliya ta biya kudin sabulu dangane da ci gaban da aka samu a kan harkokin kiwon lafiya, musamman manyan cibiyoyin kiwon lafiya da suka kunshi Asibitin kwararru ta jihar Yobe da ke Damaturu, Asibitin Koyarwa Ta Jami’ar jihar Yobe hadi da Asibitin Mata da kananan Yara.”

“Yayin da kuma abin bai tsaya nan ba, gwamnatin Gwamna Mai Mala Buni ta taka rawar gani wajen bunkasa tsarin kiwon lafiya matakin farko ta hanyar samar da cibiyar kiwon lafiya daya a kowace gunduma, babbar asibiti daya a shalkawatar kowace karamar hukuma, tare da daukar matakin amfani da yan asalin wannan jihar a matsayin ma’aikatan kiwon lafiya da basu cikakken horon sanin makamar aiki.”

“A hannu guda kuma da zakulo kwararru domin damka musu harkokin kiwon lafiya tare da alhakin gudanar dashi bisa doka da tsari.” Ya nanata.

Hoto: Dr Mohammed Gana, Kwamishina a ma’aikatar lafiya.

- Advertisement -