An yi jana’izar Iyan Zazzau, Alh Bashar Aminu, a Zariya

0
50

An yi jana’izar marigayi Iyan Zazzau, Alhaji Bashar Aminu, yau Asabar 2 ga watan Janairu, 2021, misalin karfe 10 na protected a birnin Zariya, jihar Kaduna.

Dubunnan mutane solar halarci sallar jana’iza Iyan Zazzau wanda aka gudanar da babban Masallaci Juma’a karkashin jagorancin Babban Limamin Masarautar Zazzau, Liman Dalhatu Kasimu.

Bayan Sallar Jana’iza aka garzaya da gawar mamacin kuma aka birneshi a gidansa dake Sabon Gari GRA, Aminiya ta ruwaito.

An yi jana'izar Iyan Zazzau, Alh Bashar Aminu, a Zariya

Masarautar Zazzau ta yi babban rashin da ba tayi irinta ba tun rasuwar marigayi sarkin zazzau, Alha Shehu Idris.

Ko Adashe Ne Nima Sai Nayi Naje Dubai Din nan – SadiQ Sani SadiQ

Manyan masu sarauta biyu suka mutu ranar juma’a.

Yayinda Iyan Zazzau, Aminu, ya rasu a wani asibitin jihar Legas kuma aka kai shi Zaria domin jana’iza, Talban Zazzau, Iya-Pate, ya rasu ne a Zariya bayan rashin lafiyan da yayi fama da shi.

Mai martaba sarkin Zazzau, Ahmed Bamalli, ya fara sanar da mutuwar Iyan Zazzau a shafin Tuwita, ranar Juma’a.

“Cikin bakin ciki da alhini muke sanar da mutuwar mai sarauta mafi karfi kuma Yarima mafi arziki a arewacin Najeriya, Alha Bashar Aminu, Iyan Zazzau,” yace.

What's On Your Mind?