Zamfara: Yayin Da Hankali Ya Karkata Kan EndSARS… Masu Garkuwa Sun Ci Karensu Ba Babbaka

0
112

Yayin da hankali ya karkata kan zanga-zangar EndSARS a fadin Nijeriya, masu garkuwa da mutane photo voltaic ci karensu babu babbaka, inda su ka rika addabar jama’a kauyukan Jihar Zamfara su na yi mu su dauki-daidai.

Binciken Wakilin LADERSHIP A YAU ya nuna cewa, duk da kokarin da gwamnatin Jihar Zamfara ke yi karkashin jagorancin Gwamna Bello Muhammad Matawallen Maradun na ganin an sasanta da mahara masu garkuwa da mutane da satar shanu, abin ya ci tura, don yanzun haka, maharan na kai hare-hare a sassan kauyukan jihar ta Zamfara, inda alkaluma na nuni da cewa, sama da mutane 50 ne a ka kashe a cikin sati biyu, kuma an yi garkuwa da mutane 103 a fadin jihar.

A binciken da MOBILIZED9JA A YAU ta yi, a cikin sati biyu da su ka gabata an kashe mutane 22 a garin Gidan Goga cikin karamar hukumar Maradun. An kuma kashe mutane 30 a Tungar Kwana cikin Karamar hukumar Talalan Mafara, sannan a karamar hukumar Maru an kashe mutane uku da garkuwa da mutane 53 ciki har da Hakimin garin. A garin Dankurmi kuwa an kashe mutane hudu da yin garkuwa da matar Maigarin.

Kazalika, a garin bayan Gidan Wuta da ke garin Anka an dauki mutum bakwai; maza hudu da mata biyu da kuma goyo daya. A wancan makon kuwa, an shiga kauyen Saminaka da ke gundumar Sabon Birni a Banaga ta karamar hukumar Anka, inda su ka yi wa mutane biyu yankan rago. Bugu da kari, a cikin garin Anka kuma an kama mayta uku, wadanda har kawo hada wannan rahoton ba a samu labarin inda su ke ba, kamar yadda yayansu ya bayyana wa MOBILIZED9JA A YAU.

Zamfara: Yayin Da Hankali Ya Karkata Kan EndSARS… Masu Garkuwa Sun Ci Karensu Ba Babbaka

A binciken da MOBILIZED9JA A YAU ta yi a kan halin da manoman Jihar Zamfara ke ciki na mawuyacin hali, musamman a kauyuka, shi ne na barazanar mahara wajen kwashe amfanin gonarsu, inda duk wanda ya shahara wajen noma a yanzu haka gonar ta gagare shi shigarta, inda ba ma mai gonar ba, duk wani makusancinsa wanda idan maharan su ka samu labarin ya je aiki gonar su na yin garkuwa da shi a kan sai an biya kudin fansa. Wannan shi ne kalubalen da manoma ke fuskanta a cikin wannan kaka.

MOBILIZED9JA A YAU ta tuntubi Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Zamfara, Hon Suleman Tinau Anka, kan matsalar tsaron, inda ya bayyana cewa, Gwamantin Jihar Zamfara a karkashin jagorancin Gwamna Bello Muhammad, ta amso mutane daga hannun masu garkuwa da mutane su kimanin 500, kuma yanzu haka, Gwamna Matawallen Maradun ya amso agaji daga Sufeto Janar na ’Yan Sandan Nijeriya na karin jami’an tsaro 800, wadanda yanzu haka su na cikin sassan jihar ta Zamfara.

Kwamishinan Suleman Anka ya kara da cewa, Gwamnatin Jihar Zamfara ce ke daukar nauyin Jami’an tsaron ‘yan sanda na dukkan bukatunsu, don kare rayukan al’ummar jihar ta Zamfara.

Arewa group Rues death of Northerners

Kuma a yanzu haka garuruwan da maharan su ka kai ma harin, kamar Tungar Kwana da Gidan Goga, gwamantin jihar ta aike mu su da tallafin kayan abinci da suturu da katifu da tabarmi da kuma kudi.

Hon. Anka ya tabbatar da cewa, Gwamna Matawallen Maradun ya ci alwashin kare rayukan al’ummar jihar kuma ya ba jami’an tsaro bisa umarnin gamawa da ‘yan ta’addan a duk inda su ke a fadin jihar ta Zamfara.

A ta bangaren jami’an rundunar Sojojin Kasa ta bakin Jami’n yada labarai na rundunar dakarun Sojojin SAHEL SANITY da ke da sansani a Faskari cikin Jihar Katsina, kuma sansanin da ke kula da jihohin Arewa maso Yamma, Kanar Aminu Iliyasu, ya bayyana cewa, dakarunsu na iya kokari wajen dakile ayyukan ‘yan ta’adda.

Kanar Iliyasu ya bayyana cewa, “a atisayen da rundunar ta gudanar daga 4 Satumba zuwa 25 Oktoba 2020, an hallaka ‘yan bindiga 38, yayin da kuma a ka cafke masu taimaka mu su da bayanan sirri da kayan aiki mutane 93.”

“Hakazalika, sojojin photo voltaic kwato bindigogi kirar gida guda 30 gami da harsasai kirar 7.62 mm Explicit guda 941 tare da harsasan da gajeriyar bindiga guda 5.A yayin fafatawa da ‘yan ta’addar a wurare daban-daban.”

Aminu ya kara da cewa, “sojojin photo voltaic yi nasarar kwato shanun sata 131, kananan dabbobi 154 gami da rakumi daya. Kuma mun sami nasarar ceto wadanda a ka yi garkuwa da su har mutum 108. Mun cafke masu taimaka wa ‘yan bindiga 90 gami da dillalan shanun sata uku. Haka kuma an ragargaza maboyar ‘yan bindiga 12 tare da dakile hare-haren ‘yan bindiga kan al’ummar yankin har sau 47 gami da harin satar mutane sau 31.”

“Yanzun haka dai, zaratan rundunar SAHEL SANITY na cigaba da kaiwa da kawowa a daukacin yankin, domin dakile duk wata barazana ga al’umma da kuma ganin manoma photo voltaic kwashe amfanin gonarsu ba tare da barazanar ‘yan ta’adda ba.”

A yayin da Wakilin MOBILIZED9JA A YAU ya tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sanda na Jihar, SP Muhammad Shehu, kan bayanan da su ke da shi kan halin da a ke ciki tun bayan barkewar zanga-zangar EndSARS, ya shaida ma sa cewa, zai tattara bayanai kafin ya ce komai, inda ya yi alkawarin za su sake yin magana daga bisani. To, amma har zuwa hada wannan rahoton, bai ba shi bayanin komai ba.

What's On Your Mind?