Yawan Al’ummar Sin Na Karuwa Da Kaso 0.53 A Shekara Cikin Shekaru Goman Da Suka Gabata

- Advertisement -

Yawan Al’ummar Sin Na Karuwa Da Kaso 0.53 A Shekara Cikin Shekaru Goman Da Suka Gabata

Daga CRI Hausa

Hukumar kididdiga ta kasar Sin (NBS) ta sanar da cewa, daga shekarar 2010 zuwa 2020, yawan al’ummar Sinawa dake zaune a babban yankin kasar, yana karuwa a kowa ce shekara da kason da ya kai zero.53.

Shugaban hukumar Ning Jizhe, shi ne ya bayyana haka Talatar nan, yana mai cewa, karuwar ta yi kasa da matsakaicin karuwar da ake samu a ko wace shekara na kaso zero.57 daga shekarar 2000 zuwa 2010.

Alkaluma na nuna cewa, yawan al’ummar kasar Sin, ba ya karuwa cikin sauri a cikin shekaru goman da suka gabata. Tun a shekarun 1990 ne dai, kasar Sin ta ke gudanar da kidayar jama’ar ta, bayan shekaru 10. Kuma yawan al’ummar kasar dake zaune a babban yankin kasar, ya kai biliyan 1 da miliyan 411 da dubu 780, karuwar kaso 5.38 daga shekarar 2010, kamar yadda sabbin alkaluma suka nuna.(Mai fassarawa: Ibrahim daga CRI Hausa)

- Advertisement -