Yaushe Za A Kawo Karshen ‘Yan Bindiga A Neja?

0
184

Yaushe Za A Kawo Karshen ‘Yan Bindiga A Neja?

Daga Muhammad Awwal Umar, Minna

Tsawon lokaci gwamnatin jiha da jami’an tsaro ke fadin solar kusa kawo karshen ‘yan bindiga da masu garkuwa musamman a yankunan da abin yafi kamari musamman yankunan karkara da ke kwana da ido daya.
Lamarin wanda a kullun yake kara kamari da ya kaiwa wasu karkarun zama kufai a halin yanzu musamman yankunan kananan hukumomin Rafi, Mariga da Shiroro da Munya da mafi yawan karkaru solar watse saboda fargaba da tsoron yadda ‘yan bindigar ke cin karen su ba babbaka ba tare da fargabar komai ba.
A taruka da dama gwamnan Abubakar Sani Bello ya sha bayyana fargabarsa akan yadda yake baiwa jami’an tsaro gudunmawar kayan aiki amma ta kai wasu lokuttan jami’an tsaron kan tsere saboda yadda lamarin ke gudana wanda yaki cigaba, yaki ci baya.
A cikin wannan watan mai albarka maharan solar kai munanan hare hare da ya kai ga dubban mutane zama ‘yan gudun hijira wanda kusan mata da kananan yara ke cikin halin tagayyara na rashin abinci da matsugunni mai inganci.
Irin wannan mummunar harin ya sami mutanen Kuchi da Choli zuwa Gunni da Zazzaga duk a cikin karamar hukumar Munya. karamar hukumar Rafi da lamarin ya zama tsohon labari da ya daina zama labari kasancewar kusan karkaru da dama solar watse wasu na gudun hijira zuwa wasu kananan hukumomi yayi da masu karamin karfi suna tsugunne a wuraren da gwamnati ta tanada duk da cewar ko a nan ba su tsira ba.
Dangane da karamar hukumar Shiroro kuwa, tunda daga a yankin Erene kusan wasu yankunan solar kusa zama tarihi sai a littafi ko idan ana bada labarin kafuwarsu saboda mamayar maharan da ke zama suna barje gumin su.
Jami’an tsaro da dama solar rasa rayukansu, magidanta da dama mata da kananan yara solar zama ababen garkuwa da daruruwa ke hannun maharan wanda rashin halin biyar kudin fansa yasa solar kasa sanin hakikanin matsayarsu na rayuwa.
Rahotanni solar tabbatar da cewar zuwa yanzu saboda rashin tabbas daga bangaren gwamnatin yasa tilas wasu yankunan solar fara zama da maharan dan yin yarjejeniyar ba su damar cigaba da rayuwarsu a yankunan su na haihuwa domin idan ma solar ja ba su da mafita.
Masana da dama na ganin matsayin na gwamnati na kin biyan kudin fansa ga maharan da gwamnatin ta tsayu akan shi daidai ne, domin a ra’ayin su hakan zai karya guiwar maharan na rashin samun kudaden shigar da zai ba su damar samun karin makaman da suke gudanar da aika-aikar ta su.
Yayin da wani bangaren ke kallon wannan matsayin tamkar kara jefa rayukan mutane a cikin hadari ne, maimakon lamarin yayi sauki kullun kara kamari yake domin kusan yankunan da zama a matsayin talakawa manoma kusan su lamarin ke afkama wa, da ya kai ga kusan solar raya samun matabbatar rayuwa, ban cin fargaba da tsoron da suke ciki talauci na kara samun gindin zama da ya kai ga solar fara fargabar tsayawa akan madogararsu ta rayuwa wato noma da kiwo.
Lamarin maharan ya faro kamar wasa inda suke aukawa cikin karkaru suna kwashe dabbobi, daga baya suka fara kwasar abinci, inda ta kai bayan kwasar abincin solar fara kona garuruwa. Ayyukan maharan bai tsaya nan ba, solar koma bude wuta da bindiga suna kashe mutane tare da yin awon gaba da jama’a, da ya kai ga Allah kadai yasan adadin mutanen da rayukan su ya salwanta sanadiyar ayyukan ‘yan bindigar.
Yanzu haka dai akwai sansanin ‘yan gudun hijira da dama a kananan hukumomin Rafi, Munya da Shiroro, Mariga da ke kunshe da mata da kananan yara da mazajen aure dama har yanzu wasu ba su san inda iyalan su ke ciki ba.
Yunkuri da kokarin ‘yansa kai na ganin solar karya lagon maharan da su kan su suka samu rayuwarsu ta zama abin barazana daga wasu daga cikin jami’an tsaro yasa tilas suna neman gwamnatin da ta dubi halin da suka samu kan su, saboda wasu lokuttan suna zargin wasu gurbatattun jami’an tsaro kan masu barazana na batanci da ke kai su ga garkamewa a gidajen yari da zargin suna hada kai da maharan, wanda bincike ya tabbatar kusan iyayen gijin maharan kan sakarwa gurbatattun kudade dan sakarwa yaran su mara.
Koma da me ya kamata gwamnati ta kara kaimi akan wanda ta ke da shi, wajen sanya ido ciki da wajen sanin hakikanin abinda ke faruwa, ta yadda za ta cin ma mafarkin da ta ke da shi na kawo karshen wannan mummunar lamarin.
Lokaci yayi da za a samar da dokar baiwa gwamnatin jihohi da na kananan hukumomi damar taka rawa akan matsalar tsaron da ke zama silar tafiyar rayukan jama’a, musamman samar da kayan aiki ga jami’an tsaro da ‘yansa kai ta yadda za a iya hada hannu da karfe wajen murkushe su ba tare da daukar zamani mai tsawo ba dan gudun jefa rayukan jama’a cikin kunci da talauci.

What's On Your Mind?