Yau Aka Yi Jana’izar Idris Deby

0
277

Yau Aka Yi Jana’izar Idris Deby

A yau Juma’a, 23 ga watan Afrilu ne aka gudanar da jana’izar tsohon Shugaban Kasar Chadi, Idriss Deby, wanda ya rasu a farkon mako sakamakon raunukan da ya samu a lokacin fafatawa da ‘yan tawaye a arewacin kasar.

Shugaba Deby dai ya mutu ne kwana daya bayan sakamakon zabe ya nuna shi a matsayin wanda ya yi nasara inda yake shirin soma mulki a wa’adi na shida. Ya kuma shafe sama da shekaru 30 yana mulkar kasar.

What's On Your Mind?