Yaro dan shekara 13 ya burge mutane da dama a shafukan sada zumunta bayan ya kera abin hawa da kwalin sabulu

0
241

Yaro dan shekara 13 ya burge mutane da dama a shafukan sada zumunta bayan ya kera abin hawa da kwalin sabulu

Wani dan Najeriya mai shekaru 13 ya sha ruwan yabo a shafukan sada zumunta bayan ya kera motar wasan yara da kwalin sabulu.

Matashin yaron ya kara tabbatar da cewa Najeriya gida ce ga yara masu hazaka da yawa waɗanda a shirye suke su mamaye duniya da fasaharsu.

Da yake wallafa hoton motar a shafinsa, @OmoGbajaBiamila ya rubuta:

“Wannan yaro dan shekara 13 mai hazaka ya kera wannan motar tun daga farko da kwalin sabulu. Dan Allah a yada don duniya ta ga gagarumin fasaharsa …”

Idan aka kula da hazikancinsa sosai, yaron mai shekaru 13 zai iya gina abin da Abdulmumin Adinoyi Taofiq ya gina kwanaki.

A tuna cewa Abdulmumin ya sa mabiya kafofin sada zumunta magana bayan ya gina karamin jirgin sama kuma ya tashi.

Yan bindiga sun sheke ‘yan sanda 3 a Abia, sun yi awon gaba da bindigogi

Yaron ya yada wani bidiyo a shafukan sada zumunta inda aka ga ya tashi ‘jirgin’ tare da na’urar sarrafa shi.

An jiyo sauran samari da suka hallara don shaida abin da ya faru suna ta ihu cikin farin ciki yayin da jirgin ya tashi sama.

Abdulmumin ya rubuta: “A ƙarshe na sanya jirgina ya tashi, bayan shekaru da yawa ina ƙoƙari. Na ari batirin Lipo daga hannun Victor Moses. Har yanzu ina buƙatar ɗaya ta kaina duk da cewa, ya kai 15k. #Taohan.”

A wani labari na daban, wani ‘dan mai ba uwargidar shugaban Najeriya, Aisha Muhammadu Buhari, ya fito da hotunan wata mota mai tsada da ya mallaka.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa wani yaron Dr. Hajo Sani, ya saye wata mota wanda za ace ‘son kowa, kuma kin wanda ya rasa.’

Wannan Bawan Allah mai amfani da sunan Kingdibbo a shafinsa na Instagram, shi ne ya wallafa hotunan sabuwar amaryar da ya yi.

What's On Your Mind?