Yanzu-yanzu | Gwamnatin Kano Ta Rusa Makarantar Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara

0
19

Gwamnatin Kano ta rushe inda Malam Abduljabbar Nasir Kabara ke bayar karatu kusa da Jauful Fara, da ke filin mushe.

An ɗauki lokaci ana rikici kan filin tsakanin malamin da mutane a unguwar ta filin mushe da Mallam Abduljabbar ke karatu.

(Kalli Bidiyo)Wani Bidiyon Jarumi Sadeek Sani Sadik da Matarsa Yajamasa Zagi a Shafukan sada Zumunta

Gwamnati ta ƙwace filin sakamakon koke da ta samu daga mutanen yankin, kan cewar filin mallakinsu ne.

Kimanin wata biyu kenan gwamnati ta fitar da filaye a wajen ciki har da na Malam Abduljabbar da ya yi iƙirarin gwamnatin da ta shuɗe ce ta ba shi.-BBC

Ga hotunan nan

Yanzu-yanzu | Gwamnatin Kano Ta Rusa Makarantar Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara

What's On Your Mind?