Yanzu-Yanzu: Fursunoni sunyi yunƙurin tserewa daga gidan yari a Kano

0
174

Fursunoni sunyi yunƙurin tserewa daga gidan yari a Kano

Fursunoni a gidan yari na Kano sunyi yunkurin tserewa a yammacin ranar Alhamis

Musbahu Nasarawa, kakakin hukumar kula da gidajen gyaran hali na Kano ya tabbatar da hakan

Nasarawa ya ce hargitsin ya tashi ne yayin da jami’an gidan suka yi kokarin kwace wasu haramtattun kaya daga hannun fursunoni

Jami’an tsaro, a yammacin ranar Alhamis sun dakile wata yunkuri da fursunoni suka yi na tserewa daga gidan gyaran hali na Kurmawa da ke kusa da fadar Sarki a jihar Kano, The Cable ta ruwaito.

An ji harbe-harben bindiga a kusa da unguwa da gidan gyaran halin ya ke a yayin da mutane ke shirin yin bude baki a yammacin ranar Alhamis.

Musbahu Nasarawa, mai magana da yawun hukumar gidan gyaran hali na Kano ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce wasu fursunonin sun so tada hargistsi ba su yi nasara ba.

“Mun dakile yunkurin da taimakon jami’an gidan gyaran halin,” in ji kakakin hukumar.

Nasarawa ya ce hargitsin ya tashi ne a lokacin da jami’an gidan gyaran halin suke kokarin kwato wasu haramtattun kayayyaki daga hannun wasu fursunoni.

Da farko, rahotanni da ba a tabbatar ba sun ce fursunonin sun tada hargitsi ne saboda rashin samun abinci mai kyau yayin bude baki. Don haka suka yi yunkurin fitowa su sha ruwa a waje a ranar Alhamis.

Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Fitar Da Biliyan N1.8 Don Kafa Cibiyoyin Gyaran Mota

Amma, Nasarawa, ya musanta wannan ikirarin da aka yi cewa rashin abinci mai kyau ne ya janyo hargitsin.

Ya kara da cewa a halin yanzu komai ya lafa kuma babu wani fursuna da ya tsere.

A wani labarin daban kun ji cewa ‘yan sanda a jihar Kano sun ceto wata yarinya mai shekaru 15, Aisha Jibrin, da iyayenta suka kulle ta a daki tsawon shekaru 10 a Darerewa Quaters a karamar hukumar Fagge ta jihar Kano.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata ya ce mahaifiyarta Rabi Muhammad tana hannunsu amma mahaifinta ya tsere.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata ya ce mahaifiyarta Rabi Muhammad tana hannunsu amma mahaifinta ya tsere.

What's On Your Mind?