Yanzu-yanzu: Buhari ya sallami Buratai, da sauran hafsosin tsaro, ya nada sabbi

0
24

Shugaba Muhammadu Buhari ya sallami dukkan hafsoshin tsaron Najeriya a ranar Talata, 26 ga watan Junairu, 2021, kuma ya nada sabbi ba tare da bata lokaci ba.

Mai magana da yawun Buhari, Femi Adesina, ya bayyana haka a shafinsa na Tuwita.

Hotunan Fuskokin Sababbin Hafsosin Tsaro Da Buhari Ya Nada A Yau

A cewar Adesina, Buhari ya nada Manjo Janar Leo Irabor a matsayin shugaban hafsoshin tsaro; Manjo Janar Ibrahim Attahiru matsayin shugaban Sojin kasa; RA AZ Gambo matsayin
shugaban sojin ruwa, da kuma AVM IO Amao matsayin shugaban mayakan sama.

Buhari ya sallami Buratai, da sauran hafsosin tsaro, ya nada sabbi

What's On Your Mind?