Yanzu Yanzu Buhari Ya Kaiwa Kwankwaso Ta’aziyya Rasa Mahaifin Sa Da Yayi

0
76


Shugaba Buhari Yayi Ta’aziyya Ma Kwankwaso Bisa Rasuwar Mahaifin Sa, Yace Marigayin Ya Kasance Shugaba Mai Kyau.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana ta”aziyyan sa bisa rasuwan mahaifin tsohon gwamnan jihar Kano Kwankwaso, wato Alhaji Musa Saleh hakimin Madobi.

A cikin wani sako a ranan juma’a, Shugaba Buhari yana cewa” rasuwan Musa Saleh, mun rasa daya daga cikin dattawa kuma basaraken gargajiya mai mutunci cikin kasan nan wanda ya bayar da gudumawa zuwa ga zaman lafiya da kuma hadin kan kasa ba zamu taba mantawa da shi ba har bayan rasuwan sa”.

Bisa ga Shugaban kasa, “yace marigayi Saleh ya kasance mutun ne na kwarai mai kyawawan hali wanda ya ke da tawali’u kuma mai saukin kai tsakanin su mai girma da nagarta. 

bari nayi amfani da wannan damar zuwa nuna kaduwan zukatun mu da nuna juyayi zuwa ga tsohon Gwamna Kwankwaso, Gwamnatin jihar Kano da kuma Masarautan Kano bisa rasuwan wannan Hakimin. Allah ubangiji ka gafarta masa kura kuran sa kuma ka yi masa sakayya bisa kyawawan aiyukan sa da gidan Aljannah Amin.” Shugaban kasa ya kammala. 

Mal Garba Shehu:

Babban Mai Tallafawa Shugaban kasa A Kafofin Watsa Labarai da Wayar da kan Jama’a. 

25 ga watan Disamban Shekarar 2020.

Dan Allah Kuyi Share Zuwa Fb WhatsApp Twitter Instagram and Da Sauram Soshiyal Midiya.

What's On Your Mind?