Yanzu Yanzu: Buhari Ya Bada Umurnin Bude Boda Guda (4)

0
76


Dole Uwar Naki  Wuya Mai Sa Gudu, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin buɗe iyakokin Najeriya huɗu na kan tudu da suka haɗa da Seme da Illela da Maigatari da kuma Mfun.

Mai taimaka wa Shugaba Buharin kan shafukan sada zumunta Bashir Ahmad ne ya wallafa hakan a Tuwita a ranar Laraba da yamma.

Sai dai sanarwar ba ta bayyana dalilan da suka sa aka buɗe iyakokin ba, duk da cewa ƴan ƙasar solar daɗe suna fata ganin hakan.

Amma mai bai wa Shugaba Buharin shawara kan yada labarai Garba Shehu ya cewa BBC dalilin buɗe iyakar shi ne sakamakon shawarar da wani kwamiti na musamman da shugaban ƙasar ya kafa kan matsalar rufe iyakar.

Amma kafin nan sai da aka samu hadin kai daga makwabtan kasashe kan matsalolin da suka sa aka rufe iyakokin.

A watan Agustan 2019 ne gwamnatin Shugaba Buharin ta rufe dukkan iyakokin ƙasar na kan tudu sakamakon abin da ta kira barin su a buɗe na jawo fasa ƙwaurin miyagun ƙwayoyi da maamai waɗanda suke barazana ga tsaro.

Sannan gwamnatin ta ce cikin dalilan har da ƙoƙarinta na hana shiga da shinkafa ƴar waje cikin ƙasar a ƙoƙarinta na bunƙasa noman shinkafar a cikin gida.Shugabannin ƙasashe maƙwabtan Najeriya solar daɗe suna roƙonsa da ya buɗe iyakokin.

Dukkan iyakokin da aka bayar da izinin buɗewa ɗin waɗanda suke kan iyakar ƙasar ne da jamhuriyyar Nijar da ta Benin.

Me masana ke cewa kan buɗe iyakokin?

Tuni dai masana suka fara sharhi inda Dr Abdurrazak Ibrahim Fagge, shugaban sashen nazarin tattalin arziki a jami`ar Yusuf Maitama Sule da ke Kano, ya shaida wa BBC cewa bude iyakokin shi ne mafi alheri.

“Dama bisa kuskure aka rufe iyakokin nan, maimakon haka gara a saka wasu matakan kamar su haraji da saka lasisi da rage yawan kayan da ake shiga da su, amma ba a rufe boda gaba ɗaya.

“Sannan rufewar ta janyo matsaloli d dama da su kansu gwamnatin suka ga cewa a baya-bayan nan ita cibiyar da take fitar da alƙaluman tattalin arziƙin kasa ta gao cewa an samu kma baya sosai a zango na uku na wannan shekarar a wajen cinikayya tsakanin Najeriya da ƙasashen ƙetare.

“Hakan ya jawo faɗuwa ta sama da naira tiriliyan biyu. To yanzu an zao daidai gaɓar da ita kanta gwamnati ke so ta fara shigo da tataccen mai daga Nijar, kenan babu yadda za ta ci gaba da rufe iyakoki ita kuma ana ganinta tana fita tana sayowa,” in ji masanin.

Ko kwalliya ta biya kuɗin sabulu?

Bayan cika shekara da rufe kan iyakokin ƙasar, BBC ta jiyo ta bakin wasu al’ummomin da ke zaune a garuruwan da ke kan iyakokin Najeriyar inda suka bayyana cewa kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba shekara guda bayan gwamnatin ƙasar ta rufe iyakokinta da ke kan tudu.

Sai dai hukumar hana fasa-ƙwauri, wadda ta yi ruwa ta yi tsaki wajen ganin an yi aiki da rufe iyakokin, ta bugi ƙirji recreation da irin nasarorin da ƙasar ta samu saboda matakin da ta dauka na rufe iyakokin tudu ta fuskoki daban-daban na rayuwa.

Joseph Attah, kakakin hukumar kwastam na ƙasa, a watan Agustan 2020 ya shaida wa BBC cewa da Najeriya ba ta ɗauki matakin rufe iyakokin nata wanda ya taimaka wajen inganta noma ba, to da ta fuskanci matsala ta ɓangaren abinci bayan ɓullar annobar korona, da ta tilasta wa ƙasashen duniya rufe ƙofofinsu.

“Harkar noma ta samu inganci, shi ya sa (matakin) ya rage wahalar da ake sha sakamakon zuwa koronabairus.

Miye Ra’ayoyin Ku Gameda Bude Iyakokin Nan Da Shugaban Kasa Muhammad Buhari Ya Bayar Da Umurnin Su….?

Domin Jin Ta Bakin Ku Kuyi Kasa Kan Wannan Submit Zakuga Alamar Feedback Sai Kuyi Tsokaci Kan Hakan.

Mungode.

What's On Your Mind?