Yanzu-yanzu: Boko Haram Sun Farmaki Gaidam A Jihar Yobe

0
328

Yanzu-yanzu: Boko Haram Sun Farmaki Gaidam A Jihar Yobe

Bayanai daga Gaidam dake jihar Yobe solar bayyana cewa a daidai lolacin da al’ummar musulmi ke kokarin buba-bakin azumin watan Ramadan, mayakan Boko Haram solar kai hari tare da harbin mai kan uwa da wabi a kowane bangare.

Wani mazaunin Gaidam- Malam Haruna Muhammad, ya tabbatar da cewa “Yanzu haka kowa ya shiga gida ya kulle saboda shigowar Boko Haram da yammacin nan- a daidai lokacin da ake shirin buda baki. Kuma yanzu haka karar harbe-harbe ce ke tashi kowane sashen Gaidam.”

A nashi bangaren, Kakakin Rundunar yan-sandan jihar Yobe, Abdulkareem Dungus ya tabbatar da cewa, “Mun samu rahoton cewa Boko Haram solar kai hari Geidam, kuma yanzu haka suna cikin garin, kana kuma yanzu haka sojojin sama solar kai dauki a garin.”

What's On Your Mind?