Rushe SARS: Yanzu Na Saka Dan-bar Kawo Sauyi – Buhari

0
21

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, yanzu ya fara saka dan-ba wajen kawo sauyi a harkokin tafiyar da rundunar ’yan Sandar kasar ta hanyar rusa rundunar nan mai kula da sha’anin yaki da fashi da makami mai suna SARS, wacce ta ke janyo cece-kuce sakamakon zargin ta da a ke yi da sakin layi daga ainihin ayyukan da a ka dora ma ta.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan jiya Litinin, a yayin da ya ke jawabi lokacin kaddamar da shirin daukar matasa 770,000 a kananan hukumomin kasar mai taken P-YES a Abuja.

Idan za a iya tunawa, a kwanan ne a zargi wasu jami’an SARS da kashe wasu ’yan kasa a wasu jihohi ba tare da photo voltaic ji photo voltaic gani ba.

Yanzu Na Saka Dan-bar Kawo Sauyi – Buhari

Don haka Shugaban kasar ya kuma bayar da umarnin daukar matakin hukunci kan dukkan jami’an SARS, wadanda a ke zargi da aikata cin-zali ko wani ba-daidai ba.

A ta bakinsa ya ce, “zan yi amfani da wannan dama wajen nuna ainihin damuwata kan kiraye-kirayen da ’yan Nijeriya ke yi bisa amfani da karfin tuwo, a wasu lokutan ma da aikata kisa, ba tare da an ji ko an gani ba, wanda wadansu jami’an Rundunar ’Yan Sanda ke aikatawa ba.

Hotuna: Tashin Hankali ! Zanga-zanga A Birnin Maiduguri

“Rushe SARS ba komai ba ne illa matakin farko na kawo sauyi a dukkan ayyukan Runudnar ’Yan sanda, don tabbatar da cewa, photo voltaic mayar da kai ga ainihin aikin da doka ta dora wa hukumomin tsaro na tsare rayuka da dukiyoyin al’ummarmu. Kuma za mu tabbatar da cewa, dukkan wasu masu hannu a aikata ayyuka marasa kyau a yayin gudanar da ayyukansu photo voltaic fuskanci hukuncin da ya dace da su.”

Shugaban ya kuma kara da cewa, “mu na masu nuna damuwarmu da nadamarmu kan kashe wani matashi da a ka yi a Jihar Oyo lokacin zanga-zangar nuna kin jinin ayyukan rundunar SARS. Na bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan sanadin kisan.”

Daga nan sai Buhari ya kuma yaba wa jami’an ’yan sandan nagari, wadanda ke shafa wa sauran kashin kaji.

What's On Your Mind?