Yanayin Tir Da Madalla Na Shigowar Bakin Al’adu Cikin Al’adun Hausawa Na Gargajiya

0
216

Yanayin Tir Da Madalla Na Shigowar Bakin Al’adu Cikin Al’adun Hausawa Na Gargajiya

Akwai ra’ayoyi da dama da masana suka bayar sport da shigowar bakin al’umma kasar Hausa. Wasu na ganin shigowarsu alfanu ne, wasu kuma na ganin cewa ba shi da amfani domin solar lalata al’adun da muka gada gun kaka da kakani. Bature ya kawo abubuwa da dama, amma daga ciki na dauki (three), wadanda suka yi tasiri a gun Hausawa zan yi bayan kan su, su ne:

Aski/wanzanci

Harkar noma

Silma da talabijin

Ta wadannan hanyoyi aka kawo kayan alatu iri-iri daga Turai, aka baza su a kasar Hausa, wadannan abubuwa solar canza zaman Hausawa kwarai da gaske.

Da farko hanyar jirgi da ta mota ta kawo wa al’ummomi da al’adu iri-iri kasar Hausa. Dole a saba da wasu bakin al’adun, koma a karbe su. Da kadan-kadan tasirin ya bace shi kenan, solar zama Hausa.

Kasancewar al’ada ta kuhshi duk rayuwar al’umma da suke gudanarwa, ba zai yiwu na yi tsokacin nan kan al’aduh Hausawa duka ba, saboda yawansu. Amma dai an kawo misalai da dama da wannan tasirin ya shafa.

Aski/wanzanci

Dangane da wannan sana’ar an samu tasirin bakin al’ada cikinta. A yau wani askin banza ya yadu ga matasanmu. Galibi askin yana kunshi da taswirori daban-daban dake bayyana wasu miyagun dabi’un Turawa. A yanzu ana samun masu aski da suka yi watsi da yawancin abubuwan da ma’aska ke amfani da su na “Gargajiya. Wasu kuma solar hada biyun duka, saboda ba su son watsi da abubuwan gado; wato suna askin Gargajiya da na zamani.

Ma’aska yanzu suna amfani da kayan aski da Turawa suka kawo. Wadannan kayayyakin solar hada da kilifa na aske gashi na hannu da na lantarki, da shanfo na wanke gashi, da sifirit na kashe amosani kai da dustin fauda. Dubi: Gudumawar harshen Hausa a matsayin harshen uwa

Bayan haka, suna da ire-iren aski da matasa kan yi, na kwaikwayon mawaka da ‘yan wasa na kasashen Turai da wasu nahiyoyin duniya, misali akwai askin da ake tara gashi a gaba, bayan an aske baya tas wai shi “fonk”, akwai kuma sikin kot, akwai wani aski da wani dan wasa ke yi yara suke yi wasi shi Balou Tolli. Wajen aiwatar da askin ma, ya koma kan kujera mai juyawa maimakon tabarma. Har wa yau, suna rina gashin kai zuwa launin kasa-kasa. To duk abin da aka bayyana a nan, yara da matasan Hausawa ne suka fi yi, wai gare su ya yi ne da zamani ya kawo. To “tir” da wannan al’adar.

Harkar noma

Akwai tasirin bakin al’adu kan Noma. Kayayyakin da suka yi tasirin solar hada da Tarakta (tractor) na huda da buge gona, da takin zamani iri-iri maimakon na gargajiya da habisat na kashe ciyawa, sifireya na feshin magunguna iri-iri, da na’urar shuki da girbi har ma da kwashe kayan anfanin gona ya sanya cikin buhu, baya ga wadannan an samu tasirin nan ma wajen iri, wanda ake kira da Turaci (improbed barieties) wato irin da aka kyautata. A halin yanzu. Manomanmu solar koma ga wadannan kayayyaki wajen tafiyar da harkokinsu na noma. Sai wanda bai samu na zamanin ba ne, yake amfani da na gargajiya, ko kuma kananan manomamnu. To a iya cewa “madalla” da tasirin wannan al’adar

Silima da talabijin

A zamanin da, Hausawa suna da wuraren shakatawa na gargajiya. Misali da daddare matasa kan taru a dandali ana yin wasanni iri-iri na raha da motsa jiki da wasa kwakwalwa da tatsuniya da sauransu, inda ba za ka taba samun wani abu na lalata ba, daga tarbiyya sai koyon jaruntaka. Amma zuwan sinima ya sa wadannan abubuwa solar canza an manta da su ga baki daya. Yanzu matasa solar fi mayar da hankalinsu wajen wasanni na zamani. Da rana bayan karatun da suke yi suna wasa kwakwalwa hade da wasu abubuwa na motsa jiki, da yamma kuma ba abin da ke ransu sai su je wasan kwallo, da dare kuma ko dai su je silima ko kuma kallon talabijin. A nan rayuwarsu ga baki dayanta ta nisanta daga wani abu na gargajiya, solar fuskanci zamani gadangadan. Haka kuma abin zai ta tafiya har girmansu.

Zuwan sinima kuwa ya yi babbar ilia ga al’adunmu na gargajiya. Dukkan abubuwan da ake nunawa a silima abubuwa ne wadanda suka shafi al’adun Turawa ko kuma wasu al’umma daban. Matasa na ganin irin wadannan yau da kullum, suna tunanin cewa su ne hanyar rayuwa irin wadda ya kamata su bi. Ba su san cewa wannan shiri ne kurum ba, wanda ko su wadanda suka shirya ba haka rayuwarsu take ba.

A cikin silima matasa ke sanin hanyoyin neman matan banza da ma yadda namiji ke yi da mace. A ciki kuma suke koyon shan giya da kwaya da ganye da caca iri-iri. Haka kuma suna ganin yadda ake shirya tashin hankali da rashin gaskiya da yadda ake shirya sata ko fashi da makamai ko yadda za a kashe mutum ba wahala, Suna ganin irin wadannan abubuwa kullum wata rana sai ka ga solar fara kwaikwayonsu, kowane matashi za ka samu yana da inda zuciyarsa ta karkata. To “tir” da wannan al’adar.

What's On Your Mind?