Yanayin Nijeriya: Abubuwan Sun Yi Yawa, Ina Talaka Zai Sa Kansa?

0
144

Yanayin Nijeriya: Abubuwan Sun Yi Yawa, Ina Talaka Zai Sa Kansa?

Daga Idris Aliyu Daudawa,

Allah Sarki wani al’amarin idan ya kasance musamman abinda ya shafi yankin ko sashen Arewa ne sai dai ayi sha’ani wai an cuci na kauye, sau da yawa abin ya kan daurewa bani kadai kai ba, kusan kowa na iya samun kan sa  cikin al’amarin. Muna fa da jagororinmu wadanda suka fara tun daga Kansila wanda shi ne dan Auta a mukamen siyasa, har ya zuwa Shugaban kasa, kowanne daga cikin su wadannan Shugabannin yana da ta sa gudunmawar da ya kamata ya rika badawa. Muddin kuma aka samu wani cikas alal misali idan ya ki yin shi al’amarin na Shugabancin daidai, to shi ma ya kwana da sanin cewar akwai abubuwan da zai fuskanta a matsayin sa na Shugaba, kar ya kalli ko shi karami ne domin kuwa shi al’amarin jagoranci ya wuce duk inda mutum yake kallon shi.

Na yi ita ‘yar karamar shimfidar ne saboda kuwa duk inda ruwa ya je ya dawo kwari zaya, tun farko kowa zai iya tunawa da akwai wata babbar makaranta wadda kowa ya taso sai da ya fara da ita, wannan makarantar kuma a gida take, manyan malaman sune Uba da kuma Uwa ko Mahaifi da Mahaifiya. Daga gida ne ake fara koya wa yaro tun yana dan karami wasu dabi’oi masu kyau, yayin da kuma za a nuna masu wasu babu kyau ya guje masu, masu kyan kuma ya rungume su hannu biyu duk inda ya samu kan sa. Daga nan kuma akwai al’umma na Unguwa wadanda nan ne suke zama, duk kuma lokacin da suka ga wani yaro ko yarinya daga unguwar ya kauce hanya za su sa shi a saiti. Akwai makarantu suma can ana koyar da tarbiyyar, dalilin da yasa na yi maganar tarbiyya anan  shi ne su wadanda ake amfani da su wajen tayar da zaune tsayen ai  suma suna da Iyaye, ana iya gane rawar da ita tarbiyyar take takawa, a cikin irin halin da muka tsinci kan mu yanzu.

Al’amarin rashin zaman tabbas ba yau aka fara yin shi ba, an dai fara ne sannu a hankali, har abin yanzu yanan nema ya gagari Kundila, amma kuma abinda zai daure kai shi ne me yasa ne sai Arewa abin yake yin kamari,  ana kuma da yadda za a iya kawo karshen shi al’amarin. Tun zamanin da marigayi Umaru Musa ‘Yar’adua yake Shugaban kasa ne abin ya dan fara kunno kai, wanda yanzu ma ana iya cewar har gangar jikin na shi kowa yanzu ya  gani. Abin ya fara ne daga sashen Arewa maso gabas wanda yake da Jihohi shida da suka hada da Borno, Yobe, Adamawa, Bauchi, Gombe, da kuma Taraba. Da farko dai an fi kai su hare- haren a Jihohin Adamawa Borno da kuma Yobe sai a hankali abin ya dan fara tsallakawa zuwa Gombe, har ma Bauchi ta samu nata daunin. Abin ya ci gaga har zuwa zamanin mulkin Goodluck Ebele Jonathan inda aka samu kai wani babban hari a Masallacin Juma’a na Kano inda aka kashe mutane masu yawa, haka dai abin ya yi ta tafiya, har ya kai shiga wasu Jihohi na Arewa maso Yamma wanda Kanon take ciki.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari lokacin daya hau karagar mulki a shekarar 2015 an yi tsammanin ne abin zai sauya, ashe ba, a kai ga rabuwa da Bukar bane sai  kuma aka haifi Habu, inda s kai su hare- haren  suka sauya alkibla. Sauya alkiblar ita ce yadda aka shigo da al’amarin garkuwa da mutane ana amsar kudaden fansa, satar shanu a kora su, da kashe mutane wadanda basu ji ba, basu kuma gani ba, ga kuma debe dukiyarsu. Kai da dai sauran abubuwan cin zarafin dan Adam wanda yanzu an maida shi bai zama komai ba. Zuwa ko nace tsakanin watannin  Disamba na shekarar 2020 zuwa Afrilu na 2021 an yi garkuwa da dalibai fiye da 970  kamar dai yadda wata kungiyar mai zaman kanta ta bayyana.

A Jihar Neja kwanaki biyu da suka gabata cikin wannan mako gwamnan Jihar Abubakar Sani Bello ya bayyana cewar wasu mutane daga  kauyuka fiye da hamsin daga kananan hukumomi biyar na Jihar ne, suka kauracewa wuraren da suke zama zuwa wani wurin da basu ma san inda suka dosa ba, ba kuma tabbas abubuwan da za su iya haduwa da su idan solar isa.

Zuwa halin da ake ciki yanzu tamkar ma wankin hula ne ya  kai dare, saboda yadda al’amuran suke kara jagulewa, an dade da fara lalube amma har yanzu ba  a samu wata makama ba. Irin haka ce ta faru a hedikwatar karamar hukumar Geidam mahaifar sabon Sufeto Janar na ‘yansandan Nijeriya Usman Baba Alkali. Can ma dai ‘yan Boko Haram solar kashe mutane, ya yin da kuma hakan ya sa mutane masu yawa suka bar gidajen su, zuwa wurin da basu ma sani ba.

Wadanda ake tsammanin  za su taimaka wajen hana aikata ta’addancin  garkuwa da al’umma sai ga shi an kamu su dumu- dumu suna taimakawasu masu garkuwa da jama’ar a Jihar Zamfara, duk kuma solar kasance jami’an tsaro ne a Jihar ta Zamfara. Wannan ko shakka babu akwai nuna rashin kishin kasa da kuma kwadayin abin duniya.

Abin yaki ci yaki cinyewa domin kusan kullun ana samun  wasu sababbin hare- haren da ake  kaiwa, wani abu kuma wanda ina ganin zai daurewa wasu masu karatu kai shi ne, ta yaya ake shigowa da makaman da suka hada da bindigogi da dai sauran kayayyakin aikinsu na ta’ddancin wannan shi ne har yanzu, babu wanda zai ce ya san, masu daukar nauyin wannan aikace- aiakace na kashe rayukan mutane da kuma sace dukiyoyinsu.

Al’amarin rayuwa  a yau tayi matukar tsada talaka yana matukar fuskantar shan wahala, ko kuma nace ana gasa ma shi gyada a kunba, ga dai tsadar kayayyaki, noman ma a wasu wurare idan ba sa’a ce aka yi ba, tunda damin ta fadi a wasu wuraren noman zai yi matukar wuya. Mutane suna ji suna gani za a shigo garuwansu ko kuma Unguwannin su, a kore masu Shanu, wadanda dasu ne ake yin huda kafin ayi shuka idan damina ta fadi.

Ku san idan dai ba wata rahama Allah ya sauko  ba  ana iya shiga cikin halin yunwa, duk da yake yanzu akwai wasu wuraren da abinda ya raba su da yunwar kadan ne, ko nace saura kiris. Wasu mutane an kona wuraren da suke zama an sake dukiyoyin su ko kaddarori, kamar dabbobi a kauyuka wadanda dauka su je kasuwa su sayar domin su samu kudaden da za su taimaka masu tafiyar da rayuuwa.  Halin da ake ciki yanzu wasu ko an ce masu su koma wuraren na su da suka, ba za su iya komawa ba.

Haka za a ci gaba da rayuwar ne yanzu  ku san kamar yadda mafarauta suke shiga cikin daji suna farautar dabbobi, haka masu ‘yan ta’addar suke farautar mutane, irin haka dai  ba zai haifi da mai ido ba. Saboda abin kamar yadda yake tafiya ba wanda zai ce yau ne, gobe, ko kuma jibi  al’amuran ta’addancin za su kawo karshe a Arewa. Ga kuma sauran sassan na Nijeriya kamar Kudu maso gabas, Kudu maso yamma, Kudu maso kudu, suma dai ana ta dan dauki dai- dai na garkuwa da jama’a da kuma kashe- kashe, amma basu kai abubuwan tayar da hankali da suke faruwa ba musamman a Arewa. Masu taimakawa tafiyar da wadannan hare- hare da kuma kashe- kashen jama’a su kwana da sanin cewa watarana dole ma su mutu, solar kuma san Allah ba azzalumin kowa bane, babu komai sai adalci. Wannan lokacin ne ya dace gwamnati ta dauki kwakwaran mataki wajen tauna tsakuwa domin Aya ta ji tsoro.

 

What's On Your Mind?