Yan ta’addan Boko Haram sun hallaka Soji 7, sun koresu daga barikinsu a Borno

- Advertisement -

Premiuim Instances ta ruwaito cewa akalla Jaruman Sojojin Najeriya bakwai sun rasa rayukansu bayan wani mumunan harin kwantan baunan da yan ta’addan Boko Haram suka kai musu a jihar Borno.

Sojojin da wannan hari ya shafa sune rundunar 153 Process Power Battalion dake karamar hukumar Marte, a Borno.

A cewar majiya, yan ta’addan sun kai wa sojin harin kwantan baunan ne misalin karfe 10 na safiyar ranar Litinin.

Sojojin sun yi ta maza inda sukayi kokarin dakile harin da fitittikar yan ta’addan.

Yan ta'addan Boko Haram sun hallaka Soji 7, sun koresu daga barikinsu a Borno
Mummunar gobara ta barke, gidaje 620 sun kone na ‘yan gudun hijira a Maiduguri

Amma duk da jaruntar da suka nuna, yan ta’addan sun galabi sojin “saboda basu iya juran ruwan wutan da yan ta’addan ke yi ba,” cewar majiyar.

Majiyar ta ce yanzu an mayar da sauran Sojojin dake Marta karamar hukumar Dikwa.

Kawo yanzu, hukumomi sun ankarar da rundunar Sector 3, musamman wadanda ke Baga, Cross Kauwa, Kekeno da Monguno da su kasance cikin farga.

Majiyoyi a gidan soja na nuna cewa harin ranar Litinin ne karo na uku da yan ta’addan zasu kai cikin wata guda.

A wani labarin kuwa, Shugaba Muhammadu Buhari yayi Allah-wadai da sace dalibai da ma’aikatan makarantar GSSS dake Kagara, jihar Neja a ranar Talata 16 ga watan Fabrairu.

Mai magana da yawun shugaban kasa Femi Adesina ne ya wallafa jawaban shugaban kasan a shafinsa na Fb yau Laraba da misalin karfe 11:44 na protected.

A cewar shugaban, ya samu labarin faruwar lamarin kai harin ‘yan ta’adda da ya auku cikin dare, wanda har ya zuwa yanzu ba a gano adadin ma’aikata da daliban da aka sace ba.

- Advertisement -