‘Yan Siyasar Amurka Da Ke Goyon Bayan Masu Adawa Da Kasar Sin Da Tayar Da Hankali A Hong Kong Sun Taka Doka A Fili

- Advertisement -

‘Yan Siyasar Amurka Da Ke Goyon Bayan Masu Adawa Da Kasar Sin Da Tayar Da Hankali A Hong Kong Sun Taka Doka A Fili

Daga  CRI Hausa

A cikin ‘yan kwanakin da suka gabata, wasu ‘yan siyasar Amurka solar yi maganganun da ba su dace ba recreation da hukuncin da kotun yankin musamman na Hong Kong ta yanke kan masu adawa da kasar Sin da tayar da hankali a yankin, har ma solar gabatar da bukata ta rashin tunani ta neman sakin wadannan masu aikata laifi.

Wadannan ‘yan siyasa a kwanan nan solar yi ta yin ikirarin cewa, wai suna kiyaye tsarin kasa da kasa bisa “ka’idoji”, amma a zahiri suna aikata ayyukan da suka keta dokokin kasa da kasa da kuma ka’idojin alakar kasashen duniya ne.

Irin abubuwan da suke fada ya sha bambam da abin da suke aikatawa, hakan ya fallasa ainihin burin su na tsoma baki cikin harkokin cikin gidan wasu kasashe ta hanyar fakewa da batun “‘yancin dan adam”.

Kotun yankin musamman na Hong Kong ta yanke hukunci na adalci kuma mai dacewa kan masu adawa da kasar Sin da tayar da rikici a yankin na Hong Kong, wanda ya nuna cikakkiyar ruhin bin doka na Hong Kong kuma ya amsa bukatun mazauna yankin.

Ka’idar rashin tsoma baki cikin harkokin cikin gida, wata muhimmiyar manufa ce ta Tsarin Dokoki na Majalisar Dinkin Duniya da kuma babbar ka’ida ta alakar kasa da kasa. Haka zalika ita ce babban tabbaci na kiyaye mulkin kan kasa da ‘yancin kan kasa da kuma kiyaye adalci na kasa da kasa.

Wasu ‘yan Amurka solar yi biris da wadannan ka’idojin kasa da kasa da aka ambata a baya, kuma suna ta tsoma baki akai-akai a cikin harkokin cikin gidan kasar Sin, da boye laifukan da masu adawa da kasar Sin da tayar da rikici a yankin Hong Kong suka aikata. Wannan ya bai wa duniya damar gani sosai cewa, suna buga tutocin da ake kira wai “‘yanci” da “demokradiyya”, amma ainihin burinsu shi ne hargitsa Hong Kong da hana ci gaban kasar ta Sin. (Mai fassara: Bilkisu)

- Advertisement -