Tsohon shugaban Kasa, Janar Abdusalam Abubakar ya bayyana cewa, ‘yan siyasar kasar nan na tafka babban laifi saboda yadda suke bai wa matasa kwayoyi da makamai musamman a lokutan zabe domin cimma muradunsu a siyasance.
Janar Abdulsalam ya bayyana haka ne a yayin zantawa da manema labarai kan bikin cika shekaru 60 da Najeriya ta samu ‘yancin kanta daga Turawan mulkin mallaka na Birtaniya.
Janar Abdulsalam shi ne wanda ya jagoranci mika mulki ga farar hula da ake cin gajiyarsa a yau, inda ya mika mulki ga Olusegun Obasanjo bayan ya lashe zaben da aka gudanar karkashin tsarin dimokradiya a shekarar 1999.
Kalli Bidiyon Aisha Tsamiya Ta Siyar Da Sabon Shagon Gashinta
Kodayake tsohon shugaban ya bayyana cewa, Najeriya ta samu ci gaba a cikin tsawon shekaru 60 da karbar ‘yancin cin gashin kanta daga Turawan Birtaniya.
139 total views, 2 views today
Be the first to comment