Jami’an ‘yan sanda Nijeriya solar tarwatsa wasu da ke zanga-zanga a Abuja babban birnin tarayya, inda suka harba musu hayaki mai sa hawaye.
Masu zanga-zangar na kira ne da a rushe rundunar musamman da ke yaki da fashi da makami ta SARS. Wasu daga cikin masu zanga-zangar solar shaida wa manema labarai cewa an daki wasunsu kuma an kama wasunsu.
Lamarin ya faru ne yayin da masu zanga-zangar ke tattaki zuwa hedikwatar ‘yan sandan da ke Abuja. Ko a daren jiya sai da masu irin wannan zanga-zangar suka yi zaman dirshen inda suka kwana a gaban gidan gwamnatin jihar Legas.
202 total views, 2 views today
Be the first to comment