‘Yan Sanda Sun Sake Yin Artabu Da Masu Satar Mutane A Edo

- Advertisement -

‘Yan Sanda Sun Sake Yin Artabu Da Masu Satar Mutane A Edo

Daga Mahdi M. Muhammad, Abuja

Rundunar ‘yan sanda a jihar Edo ta yi artabu da masu satar mutane, inda suka kashe uku daga cikinsu tare da kubutar da mutane bakwai da aka sace, in ji wani jami’i.

Kontongs Bello, mai magana da yawun ‘yan sanda na Edo, ya fadi haka a cikin wata sanarwa a ranar Litinin.

Ya ce, ‘yan sanda solar yi aiki tare da tawagar ‘yan banga na yankin don cimma nasarar.

Ya ci gaba da cewa, jami’an tsaron solar ci karo da wadanda ake zargin masu garkuwar ne a layin Ahor da ke hanyar Benin zuwa Lagos sannan suka yi artabu da su, inda aka kashe uku daga cikin wadanda ake zargin masu garkuwa ne. Amma bai ambata ko ‘yan sanda solar samu rauni ba a yakin.

Bello ya ce, tare da mutane bakwai da aka ceto, da kuma 13 da aka ceto a ranar Asabar da ta gabata, jimillar wadanda abin ya shafa tsakanin Asabar da Litinin solar kai 20 yanzu.

Wannan lamari na baya-bayan nan ya faru ne kimanin makonni biyu bayan da ‘yan sanda Edo suka yi wata arangama da wasu masu satar mutane a yayin musayar wuta a yayin da aka ceto mutane biyu da aka sace.

Wani jami’in ya ce, ‘yan sanda solar kuma gano kimanin Naira 200,000 daga hannun masu garkuwar a yayin lamarin na ranar 28 ga Afrilu.

Edo na daya daga cikin jihohin Nijeriya inda satar mutane don neman kudin fansa ta yi kamari. Sauran jihohin solar hada da Enugu, Kaduna, Katsina da Akwa Ibom.

A ranar Litinin, Bello ya bayyana cewa, sabuwar nasarar ita ce ci gaba da aikin gandun daji wanda Phillip Ogbadu, kwamishinan ‘yan sanda a Edo ya yi alkawarin.

Bello ya sake nanata cewa kwamishinan ‘yan sanda ya yi alkawarin ci gaba da wannan aiki kuma ba zai hakura ba har sai jihar ta kawar da masu satar mutane.

Ya ce, Ogbadu ya kuma nemi hadin kai da kawancen masu ruwa da tsaki ta hanyar musayar bayanai, musamman daga wadanda ke kusa da garin Ahor da kewaye.

- Advertisement -