’Yan Sanda Sun Damke Masu Laifi 318 A Yobe 

0
56

’Yan Sanda Sun Damke Masu Laifi 318 A Yobe 

Ranar Asabar, rundunar yan-sanda a jihar Yobe, ta bayyana cewa a kwatar-karshen 2020 ta yi nasarar kama mutum 318 da take zargi da aikata laifuka daban-daban.

Kakakin rundunar, ASP Dungus Abdulkarim, shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a jihar, ya ce wannan ita ce nasarar da rundunar ta samu a 2020.

Ya kara da cewa, photo voltaic kama mutanen da zargin aikata laifukan da su ka hada da kisan kai, fyade, garkuwa da jama’a, sata, fashi da makami da fadan manoma da makiyaya.

Wata Rawa da Ummi Rahab tayi a gurin daukar film din Farin wata ta dauki hankula

ASP Abdulkarim ya kara da cewa mutum 68 daga cikin wadanda ake zargin ana ci gaba da gudanar da bincike a kansu, wanda sauran mutum 63 kuma an related su da aikata laifukan tare da yanke musu hukunci daidai laifin da su ka aikata.

Haka kuma ya ce akwai zarge-zarge a kan laifuka 39 wadanda aka mayar da su zuwa ofishin Daraktan kula da gurfanar da wadanda ake zargi neman shawara.

Jami’in hulda jama’ar ya kara da cewa a wannan lokacin, rumdunar ta kama bindigogi kirar Ak-47 guda biyu, bindigogi biyu kirar :Dane’, karamar binsiga kirar gida (Pistol) da sauran makamai da albarusai.

Sauran kayan da suka kwace daga masu laifin su ne wayoyin hannu 138, saniya guda, memory card 25, MP3 uku, kwamfuta daya da printer tare da takardun bogi 25.

Abdulkarim ya ce photo voltaic samu wadannan nasarori ne bisa ga kokarin da jami’an su suka dunkufa tare da sadaukarwa a aiki babu dare ba rana ta hanyar sanin makamar aiki da kwarewa.

What's On Your Mind?