‘Yan Nijeriya Sun Fi Nijeriya Kudi – Obaseki

- Advertisement -

‘Yan Nijeriya Sun Fi Nijeriya Kudi – Obaseki

Daga Mahdi M. Muhammad, Abuja

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya bayyana cewa, yawancin ‘yan Nijeriya solar fi Nijeriya arziki a matsayin kasa.

Ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a Benin, yayin wani taro na Jihar, tare da sama da kungiyoyin kwararru 27.

Gwamnan, wanda ya bukaci kwararrun da su hada kai da gwamnatinsa domin fadada harajin jihar domin ba gwamnati damar sauke nauyin da aka dora mata na aiwatar da ayyuka, ya nuna damuwarsa kan albashi da kuma sauran kalubalen da jihar ke ci gaba da fuskanta, wanda ya ce ba da dadewa ba zai iya kai wa Naira biliyan 40 a shekara.

Obaseki ya fada wa kwararru sosai cewa za a bunkasa jihar da kudi daga mutanen Edo.

Ya ci gaba da cewa, “a gare mu a matsayinmu na gwamnati mu ci gaba da nuna halayen kwarai, a lokacin da yanayin da ya kawo mu cikin gwamnatin ya sha bamban, Ina ganin zai zama babban rashin adalci ga Allah da kuma mutanen Jihar Edo. Muna cikin gwamnati ne don yi muku hidima, muna so ku kasance tare da mu kuma ku sake daukaka Edo.”
“Don haka, ba tare da jajircewa da hadin gwiwar wadannan kungiyoyi na kwararru daban-daban ba, babu wani abin da za mu iya yi, domin a yanzu muna kashe kusan Naira biliyan 40 a shekara wajen biyan albashin mutane da duk hanyoyin samun kudi. A da, muna samun wannan adadin ne daga kudaden shigar mai, kuma yanzu za a biya wannan adadin ta haraji daga gare ku. Saboda haka, shin ba ku da ta fada ne? Shin bai kamata ba ku ce wani anu ba? Kuma wannan ya ce, shin ya kamata kawai ya kasance recreation da sukar gwamnati ne?
Ya kara da cewa, “gaskiya magana ce, idan ba mu gina cibiyoyi ba, idan muka ci gaba da bin hanyoyin da suka gabata, muna kokarin kera taurari da jarumai masu karfi, ba za mu samu wata makoma ba, saboda idan wadannan karfafan mutane suka mutu, to yanzu me zai faru?”
Gwamnan, wanda ya lura da cewa yanzu ba a samun kudi ga gwamnati kamar yadda ake yi a da, ya nace cewa kudin yana tare da mu ‘yan Nijeriya. ‘Yan Nijeriya solar fi Nijeriya kudi. Kudaden ‘yan Nijeriya ne za su bunkasa Nijeriya. Kudin mutanen Edo ne za su bunkasa Edo.
“Gwamnati na iya yin abubuwa da yawa kuma kun ga abin da muke kokarin yi da kananan albarkatun da muke da su. Na san yadda za mu iya cimmawa. Akwai bukatar dukkan masu ruwa da tsaki su canja halayyarsu wajen bayar da gudummawa ga shugabanci na gari,” in ji shi.

- Advertisement -