Amaechi – Yan Nijeriya Na Amsar Dala 36,000 Daga Haramtattun Kasuwancin Tashoshin Ruwa

0
46

Yan Nijeriya Na Amsar Dala 36,000 Daga Haramtattun Kasuwancin Tashoshin Ruwa

Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya fusata ta yadda ake ci gaba da samun haramtattun kasuwancin tashoshin ruwa a Nijeriya. A cewar ministan, mutane suna amfani da sunan kamfanoni inda suke amsar dala 1,200 a duk kullum daga haramtattun kasuwancin tashoshin jiragen ruwa a kasar nan. Ya bayyana hakan ne wajen taron ranar murnar tashoshin jiragen ruwa ta Duniya ta shekarar 2020 wanda ya gudana a otal din Eko Resort and Suites da ke cikin Jihar Legas. Ministan ya bayyana cewa, yana da kyau a kawo karshen wannan lamari.

Yan Nijeriya Na Amsar Dala 36,000 Daga Haramtattun Kasuwancin Tashoshin Ruwa

Ya ce, “akwai matsaloli masu yawan gaske a bangaren tashoshin jiragen ruwa. Matsalolin kuwa su ne rashin tsaro.
“A yau muna samun mutumin da ke kulla kawance da sojoji wajen samun kudade wanda suka kai na dala 1,200 a duk kullum ta amfani da sunan kamfanoni.

Karanta: Masu hakar Mai da Gas sun yi asarar Naira Biliyan 320

“Mutum guda daya ke ci gaba da kulawa da wannan kasuwanci tare da samun goyan bayan wasu ma’aikatu.”
Ya zargi masu ruwa da tsaki da suke hada kai da irin wannan mutumi. Ya bayyana cewa, babu wanda ke da ikon tsayar da minista wajen kawo karshen haramtattun kasuwancin bakin teku.

What's On Your Mind?