‘Yan Nijeriya Ku Yi Addu’ar Zaman Lafiya Ga Kasa, In Ji Hukumar NOA

- Advertisement -

‘Yan Nijeriya Ku Yi Addu’ar Zaman Lafiya Ga Kasa, In Ji Hukumar NOA

Daga Mahdi M. Muhammad, Abuja

A yayin da ‘yan Nijeriya suka bi sauran kasashen duniya wajen gudanar da bikin karamar sallah, wanda ke nuna karshen azumin watan Ramadana, Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta kasa (NOA) ta yi kira ga ‘Yan Nijeriyan da su ci gaba da yin addu’a domin neman zaman lafiya mai dorewa, tsaro da kuma habakar tattalin arzikin kasar.

Shugaban hukumar, Dakta Garba Abari, ne ya bayyana hakan a cikin wani sakon Sallah da ya raba wa manema labarai ta hannun Mataimakin daraktansa na yada labarai, Mista Paul Odenyi, ranar Litinin a Abuja.

Ya bukaci al’ummar musulmi su rike darussan rashin son kai, da’a da kuma ibada daga wannan watan da aka kammala na Ramadan, don karfafa imaninsu tare da yin addu’ar zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankali na al’ummarmu.

Abari ya kuma yi kira ga al’umma da su ci gaba da yin addu’a ga jami’an tsaro da kuma gwamnati mai ci, a kokarinta na kawo sauye-sauyen da ake nema a cikin al’umma.

Shugaban NOA din, ya umarci dukkan ‘yan Nijeriya da su kasance masu bin doka da oda tare da rungumar dabi’ar kyautatawa, hakuri da kuma ladabtar da kai kamar yadda annabi Muhammad ya koyar, domin zaman lafiya a tsakanin dukkan ‘yan Nijeriya, ba tare da la’akari da bambancin addini, kabila da siyasa ba.
Yayin da yake yiwa al’ummar Musulmi barka da sallah cikin farin ciki da annashuwa, Shugaban ya bukace su da su kiyaye ka’idojin annobar Korona ta hanyar bin dokoki na kariya yayin bikin Sallah.

- Advertisement -