‘Yan Majalisa Sun Nemi A Dage Kidayar 2021

- Advertisement -

‘Yan Majalisa Sun Nemi A Dage Kidayar 2021

Daga Sulaiman Ibrahim

Majalisar wakilai ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta dage shirin kidaya yawan jama’a da gidaje da za a yi a shekarar 2021 da hukumar kidaya ta kasa (NPC) ta shirya.

Kiran ya zo ne bayan amincewa da kudirin da ke da matukar muhimmanci ga kasa wanda dan majalisar mai wakiltar mazabar Bosso / Paikoro na Tarayyar Jihar Neja, dan majalisar wakilai Shehu Beji ya gabatar a zauren majalisar a ranar Laraba.
Yayin gabatar da kudirin, dan majalisar ya ce, abubuwa da dama za su hana gudanar da aikin wanda zai shafi ingancin alkaluman da za a samu.

Ya kara da cewa, samun nasarar gudanar da aikin zai kasance cikin hadari saboda illar rashin tsaro ga ‘yan Nijeriya mazauna sassan kasar da dama wadanda suka rasa muhallansu ko kuma halin rayuwarsu ta yau da kullun ta rikice.

Beji ya bayyana cewa, ba za a iya tabbatar da tsaron masu kidayar ba a yawancin sassan kasar nan da matsalar tsaro ta addaba.

- Advertisement -