‘Yan Kungiyar Kwadago Sun Yi Fatali Da Rage Albashi A Jihar Ekiti

- Advertisement -

‘Yan Kungiyar Kwadago Sun Yi Fatali Da Rage Albashi A Jihar Ekiti

Daga Idris Aliyu Daudawa

kungiyar kwadago ta Jihar Ekiti ta ki amincewa da wani shirin da gwamnatin Jihar take yi na  sake daukar wani mataki kan mafi karancin albashi, domin ba za ta ci gaba da biyan mafi karanci Naira 30,000 ba.

Su dai shugabannin kungiyar kwadagon, waadda ta kunshi kungiyar kwadago ta kasa  (NLC), kungiyar kwadago (TUC) da kuma kwamitin sasantawa (JNC), solar   yi wani zama ne na sirri da Gwamna Kayode Fayemi, inda suka tattauna irin  halin da tattalin arzikin Jihar yake ciki, inda kuma suka yi kira  da shi cewar ya turawa manyan makarantun Jihar kudadensu,

A wata sanarwar da take dauke  da sa hannun Shugaban kungiyar kwadago ta Jihar, Kolapo Joshua Olatunde; Shugaban TUC, Sola Adigun da Shugaban kwamitin sasantawa, Kayode Fatomiluyi, bayan taron, kungiyoyin kwadagon solar yi bayanin cewar ba suyi na’am da duk wani matakin da za a dauka ba, wanda daga karshe zai kara sa ma’aikatan su tagaiyar.

A  wani al’amari kuma wanda na daban ne a jiya ne gwamnan,  ya kaddamar da wani kwamiti na mutum tara wanda zai bada shawara kan matakin da za a dauka kan, tsarin bayar da  tallafi wanda zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin masu karamin karfi da kuma mabukata a Jihar.

Lokacin da yake kaddamar da kwamitin a Ado Ekiti gwamna Fayemi, wanda shi ne zai kasance tamkar wani mabudi ne, na shi tsarin da za a aiwatar wanda kuma yana da niyyar taimakawa manoma, masu sana’ar hannu, masu kanana da kuma matsakaitan masan a’antu wadanda , lokacin da yake kaddamar da mambobin kwamitin a Ado-Ekiti, ya yi kira da cewar su yi la’akari da matsalolin da suka shafi tattalin arziki daya shafe su,musamman ma sanadiyar cutar annobar Korona.

Shi dai wannan kwamitin yana karkashin shugabancin kwamishinan kudi na Jihar Femi Ajayi, a cewar gwamnan, zai tsara su hanyoyin da za abi, wadanda kuama aka san, za su taimaka gwamnatin Jihar ta amfana daga sji tsarin Bankin duniya na kawo tallafin cutar annobar Korona.

Gwamnan ya yi kira da su ‘yan  kwamitin da su nuna  matukar jajircewa, gogewa, da kuma nuna gaskiya da kwarewar, wanda zai tabbatar da kyakkyawan hadin gwiwa wanda za a karfafa shi ya kuma  dore.

Shi ma  a nasa  jawabin, Ajayi ya yaba wa gwamnan kan tabbatar da cewa duk bangarorin da wannan annoba ta shafa an yi la’akari da su sannan kuma  ya yi alkawarin  kwamitin  zai  yi aiki tukuru domin cimma nasarar da ake bukata, a dukkannin abubuwan da suka sa a gaba.

- Advertisement -